Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Talata

1 Maris 2016

18:48:09
738301

Ba'a kafa kwamitin binciken hukumar kare hakkin dan adam NHRC bisa ka'ida ba

Harkar Musulunci a Najeriya ta yanke duk wata alaka da Kwamitin binciken da Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa (NHRC) ta kafa dangane da zargin da aka yi wa ’yan uwa na Harkar Musulunci da kai hari kan tawagar Hafsan-Hafsoshin Sojojin tarayyar Najeriya a garin Zariya a ranar 12 ga watan Disamba, 2015.

BA A KAFA KWAMITIN BINCIKEN NHRC BISA KA’IDA BA

Harkar Musulunci a Najeriya ta yanke duk wata alaka da Kwamitin binciken da Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa (NHRC) ta kafa dangane da zargin da aka yi wa ’yan uwa na Harkar Musulunci da kai hari kan tawagar Hafsan-Hafsoshin Sojojin tarayyar Najeriya a garin Zariya a ranar 12 ga watan Disamba, 2015.

Harkar Musuluncin ta yanke hukuncin rashin ci gaba da tarayya da kuma bayyana gaban wannan kwamitin bisa dalilai ne kamar haka:

Na farko, a yayin kafa wannan kwamitin, wa’adin Majalisar gudanarwar wannan hukumar ya kare, kuma a dokar gudanarwar wannan hukuma, babban Sakataren wannan hukuma ba shi da ikon karbar wani korafi ko koke na cin zarafin dan Adam daga wani mutum, jama’a ko kungiyoyi.

Na biyu, ba mu gamsu da tsarin tafi da aiki da wannan hukuma ke bi ba kan takardar koken da aka gabatar gare ta. Haka nan kuma ya zama wani abu ba saban ba da ya zama mun kasa samun damar yin gaba da gaba da mai koke a kan mu don mu tabbatar da irin gaskiyar zarge-zargensa.

A kan haka, tuni mun aika wasika ga Tony Ojukwu Esq, Shugaban wannan kwamiti na bincike na Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da ke Lamba, 19 titin Aguiyi ironsi Maitama, Abuja, dangane da wannan korafi namu.

Idan za a iya tunawa dai ba da jimawa ba bayan kaddamar da harin a kan Harkar Musuluncin, Hafsan-Hafsoshin Sojojin Najeriya ya garzaya zuwa hukumar NHRC ya shigar da koken cewa wai an yi yunkurin hallaka shi.

Daga bisani ne ita kuma Harkar Musuluncin ta mika bayaninta ga Hukumar dangane da wannan korafi na shugaban sojoji mara tushe ballantana makama.

Bisa wannan yanayi na rashin adalci da kin gaskiya da ya bayyana daga wannan kwamiti na bincike, muna shelanta cewa mun yanke duk wata alakarmu da wannan kwamiti dangane da wannan al’amari.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA
SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
08050786093
25/02/2016