Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Lahadi

21 Faburairu 2016

17:19:33
736162

Takardar da aka raba a lokacin muzaharorin #A saki Malam a yau Lahadi

Watanni biyu da suka wuce, musammatan ranar Asabar 12 ga Disamba, 2015, rundunar sojin Nijeriya ta aiwatar da abin da za a fi bayyana shi da kisan kiyashi a kan fararen hular da ba su dauke da makami, wato ‘yan uwa musulmi Almajiran Malam Ibrahim Zakzaky (H)a Zariya, jihar Kaduna. Irin mummunan ta’addancin da .

BA ZA MU MANTA DA TA’ADDANCIN ZARIYA BA

Watanni biyu da suka wuce, musammatan ranar Asabar 12 ga Disamba, 2015, rundunar sojin Nijeriya ta aiwatar da abin da za a fi bayyana shi da kisan kiyashi a kan fararen hular da ba su dauke da makami, wato ‘yan uwa musulmi Almajiran Malam Ibrahim Zakzaky (H)a Zariya, jihar Kaduna. Irin mummunan ta’addancin da sojojin nan suka yi sanannen abu ne ga kusan kowa da kowa, amma za a iya bayyana shi da cewa wani abu ne da aka yi wanda ba a taba yin irin sa ba a ‘yan shekarun nan, don kuwa babu wani wuri a duniyar nan da aka samu sojojin gwamnatin wata kasa da suka kashe fararen hula sama da dubu guda cikin awanni 48, in ba a Zariya ba. Banda wannan kuma ana tsare da daruruwan bayin Allah da suka hada da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky.

Mun fito ne a yau don mu tunatar da ’yan uwan mu ’yan kasa cewa wannan tsararren kisan gillar da aka yi wa rayukan mutane a Zariya ba fa za a iya mantawa da shi ba, saboda wadanda sojojin nan suka kashe ba bakin haure ba ne, ’yan kasa ne da aka san danginsu da garuruwansu, amma kuma aka take hakkinsu da tsarin mulki ya sahhale musu.

Bayan harin da sojojin suka kai, an yi ta gabatar da dalilan yin hakan daga gwamnatin jihar Kaduna, musamman ma dai ita rundunar soja, a kokarinsu na ba da hujja ga abin da babu hujjar yin sa. Amma idan aka dubi irin tuhume-tuhumen da aka yi wa ’yan uwa na harkar Musulunci da ake tsare da su a gidan kurkukun Kaduna, sai a ga gaskiya ta yi halinta kan matsayarmu ta farko cewa wannan kisan kiyashin da aka yi ba shi da dangantaka da tare hanya ko yunkurin kisan babban Hafsan sojin Nijeriya, amma wani abu ne da wasu da suke da matsananciyar gaba da Harkar Musulunci suka aiwatar. Don haka ga wadanda suka yarda da labarin kanzon kuregen da rundunar sojin Nijeriya ta fitar kan lamarin, sai mu ce to me ya sa ba a ambaci tare hanya da yunkurin kisan babban Hafsan sojin Nijeriya cikin tuhume-tuhumen ba? Amsar a sarari take cewa, saboda ba wani abu makamancin haka da ya auku a wannan rana da sojojin suka kai hari. An dai fade su ne don a wawitar da hankulan jama’a daga gaskiyar manufar makiya Harkar Musulunci.

To, yanzu ga shi watanni biyu sun wuce amma jami’an tsaro sun kasa gabatar da ko da tuhuma guda daya kacal a kan Shaikh Zakzaky, alhali kuwa sanannen abu ne ga manazarta harkokin shari’a cewa, ya saba wa tsarin mulki da kuma duk wata doka, a tsare wanda ake zargi a yayin da ’yan sanda ke fafutukar neman hujjojin aikata laifin da ba su sam. Shi ya sa muke ganin wajibi ne mu yi kira ga Hukumomi da su hanzarta sakin Jagoranmu tunda ’yan sanda ba su da wata shaidar da ke nuna cewa ya yi wa wata doka karan tsaye.

Abin haushi ne da takaici cewa wadanda ya kamata su fuskanci tuhuma sune kuma suke riya cewa su aka zalunta. Ji fa yadda Gwamnan jihar Kaduna ya ba da umurnin a kawar da duk wasu shaidu da ke nuna irin ta’asar da sojoji suka yi ta hanyar rusa wuraren da aka aikata laifukan yaki a cikinsu da kwashe duk baraguzan wurin, amma ya dawo wai shi ne zai binciki dalilan aukuwar lamarin na kusa da na nesa a Zariya. Ji fa yadda babban Hafsan rundunar soja sukutum da guda ya fito yana fadin wai sojojinsa mutum bakwai kawai suka kashe, alhali ga tulin hujjoji na bidiyo da hotuna da sam ba za a iya musanta su ba, na irin rashin imanin da sojoji suka nuna a Zariya.

Don haka  muke sake kira ga dukkan wanda ke yi wa Nijeriya fata nagari da ya mike tsaye kan wannan rashin adalci da gwamnatin Tarayya ta aiwatar a Zariya, saboda idan aka kyale abin da ya faru ya wuce ba tare da an yi masa kule ba, to za a iya sake maimaita shi kan wasu ’yan Nijeriyan a wani wurin daban. Hakika wadanda suke kisa da cin zarafi ba gaira ba sabat ba su cancanci a damka musu alhaki tafiyar da ragamar mulki ba.

A karshe, muna kira da a saki Jagoran Hakar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky ba tare da wani sharadi ba, tare da sauran ’yan uwa da ake tsare da su a gidajen yari, hannun Sojoji,Yan Sandals da sauran jami'an Tsaro na farin kaya. Haka nan kuma a ba mu gawawwakin ’yan uwanmu da sojoji suka kashe mu yi musu sutura,kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Aminci ya tabbata ga wadanda suka bi gaskiya.

Sa hannu:
Abdulhamid Bello
20/02/16