Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Lahadi

21 Faburairu 2016

17:14:37
736160

Rahoton hotunan muzaharar # A saki Malam a birane daban daban a Nigeria

A yau Lahadi 21 ga watan Fabrairu 2016 ne al'ummar musulmi 'yan uwa a birnin Zariya da sauran manyan birane a fadin Nigeria suka ci gaba da gabatar da muzaharori inda suke kiran da #A saki Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Masu gangamin sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

An gabatar da muzaharorin ne a garuruwan zariya, Kano, Katsina, Yola, Bauchi, Potiskum, Daura, da sauran su.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288