Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Jummaʼa

19 Faburairu 2016

18:47:05
735801

Dole a binciki alkalin kotun majistire ta daya dake titin Ibrahim Taiwo a Kaduna

Tun bayan takardar gayyata da Hukumar binciken da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ya ba wa Harkar Musulunci a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2016, yana da kyau a sani cewa har yanzu hakarmu ba ta cimma ruwa ba na samun damar ganawa da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky. Ko a ranar 8 ga watan Fabrairu,

TAKARDAR MANEMA LABARAI
HAR YANZU AN KI BA LAUYOYINMU DAMAR SU GANA DA SHAIKH ZAKZAKY

Tun bayan takardar gayyata da Hukumar binciken da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ya ba wa Harkar Musulunci a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2016, yana da kyau a sani cewa har yanzu hakarmu ba ta cimma ruwa ba na samun damar ganawa da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Ko a ranar 8 ga watan Fabrairu, 2016 sai da Lauyoyin Harkar Musulunci da suka hada da babban Lauya Barissta Femi Falana (SAN) da Barista Festus Okoye suka rubuta takarda zuwa ga Sufeto-Janar na ‘yan Sanda a kan suna bukatar a ba su damar su gana da Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem yaqoub Zakzaky, amma ina shiru ka ke ji har yanzu ba a ba su wannan dama ba.

Kasancewar sa taskar bayanai na Harkar Musuluncin, kokarinmu ko bukatar mu ta son ganawa da shi domin samun shawarwari a kan yadda za a fuskanci wannan yanayi da ake ciki muhimmin al’amari ne. Amma kuma sai ga shi dukkanin kokarin mu na mu samu damar ganawa da Shaikh Ibraheem Zakzaky kamar yadda Harkar Musuluncin ta bukata abin ya ci tura, domin kuwa hukumomin da suka dauke shi kuma suke tsare da shi ba bisa doka ba sun ki ba kowa damar ya ziyarce shi.

Saboda haka, Harkar musulunci a Najeriya tana tabbatar da cewa ya zama dole a ba ta damar ganawa da Jagoranta Shaikh Ibraheem Zakzaky kafin ta yanke hukuncin cewa ko za ta mika bayananta ga Hukumar binciken da aka kafa. Dalilinta kuwa shi ne Shaikh Ibraheem Zakzaky shi ne Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, shi ne ke magana a madadin Harkar Musuluncin kuma shi ne taskar bayanai na Harkar Musuluncin.

Bisa la’akari da irin girman abin da ya faru a garin Zariya a tsakanin ranekun 12-14 ga watan Disamba, 2015 da kuma abin da ya biyo bayan nan daga Gwamnatin Jihar Kaduna, ’yan uwa na Harkar Musulunci suna ganin ya zama tilas Lauyoyin Harkar Musulunci su gana da Jagoran Harkar Musuluncin domin samun umarni tare da karbar bayanai daga gare shi kafin karewar lokacin gabatar da takardar koken.

Idan za a iya tunawa a ranar 12-14 ga watan Disamba, 2015 ne Sojojin Najeriya suka kaddamar da tsararren harinsu a kan Harkar Musulunci a garin Zariya wanda ya jaza rasa rayukan dimbin’yan uwa na Harkar Musuluncin wadanda ba su dauke da makami. Bayan kisa ta hanyar harbi da bindiga, sojojin sun kuma kashe wasu ‘yan uwan ta hanyar Konawa da wuta wadanda suka hada da Mata da Kananan yara. Haka nan kuma sun yi wa wadanda suka kashe din kabarin bai-daya tare kuma da dauke Jagoran na Harkar Musuluncin.

Wannan al’amari ya jaza kiraye-kiraye a kan a gudanar da bincike dangane da wannan abu da ya faru, wanda hakan ne ya sabbaba gwamnatin jihar Kaduna ta kafa Hukumar bincike wanda ta bta sati shida {6} ta gabatar da rahotonta tare kuma da shawarwari.

Tuni dai Harkar Musuluncin ta bayyana rashin amincewarta da wannan Hukumar kasantuwar wasu Mambobin kwamitin suna da tsananin Kiyayya da Harkar Musuluncin, da kuma mai da Harkar Musuluncin Sanuwar ware a cikin Hukumar tare kuma da rashin sanya wakilcin Mambobin rajin kare hakkin bil Adama na Kasa ko Kasa da Kasa a cikin wannan Hukumar.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI
08050786093
17/02/2016

 

TAKARDAR MANEMA LABARAI
YA ZAMA DOLE A BINCIKI ALKALIN KOTUN MAJISTIRE TA DAYA DA KE IBRAHIM TAIWO ROAD KADUNA

Ya zama dole mu kara bayyana ra’ayinmu dangane da ’yan uwa na Harkar Musulunci da har yanzu ake tsare da su a babban gidan yarin da ke garin Kaduna suna zaman jiran shari'a. Mun yanke shawarar mu kara magana a karo na biyu dangane da wannan tsarewa da ake yi masu saboda saba doka da ke tattare da yadda aka yi hakan da kuma keta tsarin mulki da tsarin ka'idojin aiki da Alkalin kotu na daya da ke Ibrahin Taiwa Road, Awaal Umar ya yi.

1. A ranar 17 ga watan Disamba, 2015 Rundunar ‘yan Sanda ta gabatar da takardar farko akan koke dangane da ’yan uwa na Harkar Musulunci da ake tsare da su. A sakon farko na wannan takarda KMD/188x/15 ta nuna akwai adadin mutane 34 da ake zargi. A sako na biyu kuma KMD/189x/15 ya nuna akwai adadin mutane 79 da ake zargi. A bangare na uku na ruhoton kuwa ya nuna akwai adadin mutane 90 da ake zargi. Shi kuwa bangare na hudu na wannan takarda nuna cewa ya yi akwai adadin mutane 10 da ake zargi. Kuma mafi yawancinsu suna cikin wadanda aka kama ne a garin Kaduna a ranar 16 ga watan Disamba,2015. Bangare na biyar kuwa na wannan ruhoton KMD/204x/15 nuna cewa ya yi akwai adadin mutane 49 da ake zargi.

2. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ba su kai wadannan mutane da ake zargi ba gaban kotu, haka nan kuma Alkalin kotun Majistire ta daya da ke Ibrahim Taiwo Road, Awaal Umar bai bukaci ganin ko da mutum daya daga cikin wadanda ake zargin ba kafin ya sanya hannu a bisa takardar tsarewar tasu, a inda kai tsaye aka yi gidan yari da su daga Barikokin ‘yan Sanda. Alkalin kotun Majistire ta Kaduna ya sani cewa abin da ya yi ba daidai ba ne kuma ya saba wa Kundin Tsarin Mulkin Kasar nan.

3. Kuma bisa dogaro da rashin bin Ka'idar aiki da doka tun asali ya sa wannan dai Alkalin kotun ya zauna a cikin gidan kukukun Kaduna domin ya daidaita abin da ya yi a baya na saba wa doka na gabatarwa da tsare wadanda ake zargi, kuma abin da ya yi zaton ya yi ke nan a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2016..

4. Wannan rashin gaskiya da aka tafka ta ja za Alkalin Kotun Majistiren ya kasa bayyana yadda aka yi wasu ’yan uwa na Harkar Musulunci guda 4 suka tsinci kan su a cikin gidan yarin na Kaduna, wadanda dukkanin su babu sunayensu a cikin takardar rahoton da Rundunar ‘yan Sandan ta gabatar tunda fari, wato FIR. Wadannan mutane guda hudu kuwa su ne: Nasiru Umar, Auwal Abubakar, Ibrahim Abdulhamid da kuma Zaharadden Abdul’aziz. Maimakon kuma ya dakatar da wannan rashin bin doka, sai Alkalin kotun Majistirin ya ba Jami’an ‘yan Sanda umarnin su sanya sunan wadannan mutane a cikin takardar rahotunsu.

5. Haka nan kuma mun rasa dalilin da ya sanya Alkalin kotun Majistiren ya daga sauraron bukatar neman belin da aka gabatar masa zuwa 29 ga watan Maris, 2016 bisa umarnin da ya saba doka da ya ce ya samu daga Hukumar bincike cewa kada ya bayar da belin wadanda ake zargin har sai Hukumar ta kammala zamanta.

MATSAYARMU DA KUMA BUKATUNMU

1. Alkalin Alkalai na Jihar Kaduna ya gudanar da bincike dangane da abin da Alkalin Kotun Majistire ta daya da ke Ibrahim Taiwo Road Kuduna ya gudanar da aiki ba bisa ka’ida ba ta hanyar Sa hannu a takardar tsare wadanda ake zargi tun kimanin watanni uku ana tsare da su kafin ya sanya hannun ba da umarnin tsarewar tasu.

2. Ya zama dole babban jami’i mai kula da gidan yari ya gudanar da bincike domin gano yadda aka yi kuma yaushe da kuma dalilin da ya sanya mutane hudu daga cikin wadanda ake tsare da su suka sami kansu a cikin gidan yarin ba tare da gurfanar da su gaban Shari’a kuma ba tare da samun wata takardar shaida wadda ta bayar da damar a tsare su ba.

3. Muna da tabbacin cewa abu ne wanda ya saba wa doka, hankali da kuma kundin Tsarin mulkin Kasa, a ce wai Alkalin kotun Majistire da ke Ibrahim Taiwo road Kaduna ya ba ‘yan Sanda shawarar su sanya sunayen ‘yan uwan mu guda hudu wadanda babu sunayen su a farkon lamarin. Don haka mu na kira da a saki Nasiru Umar, Auwal Abubakar, Ibrahim Abdulhamid da kuma Zaharadden Abdul’aziz ba tare da gindaya masu wani sharadi ba.

4. Muna bukatar Alkalin Alkalai na jihar Kaduna da Hukumar Shari’a ta Jihar Kaduna su gudanar da bincike domin gano yaushe da yadda aka yi Alkalin kotun Majistiren ya samu wasikar da ta umurce shi da dage yanke hukunci kan bukatar neman beli da aka gabatar ma shi a ranar 14 ga watan Janairu, 2016, sai kuma kawai ya dage yanke hukunci kan haka zuwa 29 ga Maris, 2016 bisa wasu dalilai da suka saba wa doka kuma marasa kan gado.

5. Muna bayyana cewa ya zama dole a ba wa ’yan uwa na Harkar Musulunci hakkin na bin ka'ida kan komai za a yi musu. Ana tsare da ’yan uwa na Harkar Musulunci ne a gidan yari ba tare da tuhumar su da wani laifi ba. Alhali ya saba wa doka da kuma kundin tsarin mulki ya zama ana ci gaba da tsare wadanda ake zargi domin ba wa Jami’an ‘yan Sanda damar samo shaidun da babu su.

6. Muna bukatar a saki ’yan uwa na Harkar Musuluncin ba tare da gindaya masu wani sharadi ba, idan jami’an ‘yan Sanda ba su da wata hujja takawa ko karya wata doka da suka yi.

7. Muna dagewa cewa ’yan uwa na Harkar Musuluncin su ne aka zalunta a wannan al’amari da ya faru, amma kuma sai ga shi wadanda ya kamata a hukunta da aikata laifin, suna kokarin nuna cewa su ne aka zalunta.
SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI
08050786093
17/02/2016

Fassara daga Zaharaddeen Sani Malumfashi