Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Litinin

15 Faburairu 2016

16:41:56
735104

Sojoji sun yi amfani da iska mai guba a lokacin hare-haren da suka kai a Zariya

Ina gida muka sami labari sojoji sun zagaye Husainiyya Bakiyatullah da misalin 2:30 na rana. Da yake ni haris ne, ban tsaya jiran wani umarni na in tafi ko in tsaya ba, Kasantuwar na sha jin Malam Turi yana cewa da zarar kaji ance sojoji sun kai hari Gyallesu ko Husainiyya, ko wani waje na Harka Islamiyya,

Ina gida muka sami labari sojoji sun zagaye Husainiyya Bakiyatullah da misalin 2:30 na rana. Da yake ni haris ne, ban tsaya jiran wani umarni na in tafi ko in tsaya ba, Kasantuwar na sha jin Malam Turi yana cewa da zarar kaji ance sojoji sun kai hari Gyallesu ko Husainiyya, ko wani waje na Harka Islamiyya , ba bukatar jiran izini.

Sai kawai muka kama hanya mu 15 muka tafi. Mun je daidai Fly-over sai muka ga ba hanya sojoji sun rufe. Mun yi tunanin idan muka yi yawa , zamu iya tunkararsu mu bude hanya mu wuce. sai muka canza shawara muka koma ta Hanwa, muka je Dan magaji muka shiga Gyallesu.

Mun je Gyallesu dab da Magriba. Ina cikin mutane 12 da suka shiga cikin unguwar don ganin halin da ake ciki . Ina tafiya na hadu da wasu sojoji guda uku suna sayen taba a wani shago, ni ma sai na sayi tom-tom a wajen. Da suka taho na dan biyosu a baya, sai naji suna tattaunawa a tsakaninsu cewa da Malam yaje abuja da ya hutar dasu. Da yake an tsara zaije Abuja ranar asabar 12/12/15 domin halartar taron Maulidin Mujaddadi Shehu Umsman Dan Fodiye.

Naji suna cewa da yaje Abuja da abubuwan da ake tunanin za a yi anan da acan aka yisu. Naji dayan yana cewa "Nura kai zaka iya harbin mata da kananan yara kamar yadda oga yace muyi ?"
Sai yake cewa ko an fara operation din nan sai dai mu rika harbin sama. Kafin in koma gidan Malam har naji sun fara Harbe-harbe da misalin 10:30 daidai.

Hankalin mu ya koma ga wadanda aka harba, muna tunkararsu dan mu hanasu isowa ga gidan Malam.

Da yake rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke, amma harsashi yayi ta bi da gefe da saman kaina saboda kwaso gawarwaki da muke yi.

Tun muna kawowa muna kirgawa, har kirgen ya gagara. Idan muka kawo gawa muna sa mata lamba, idan an san sunan sa sai a rubuta a manna a jikinsa, sai mu daure a kafarsa. Lokacin da lissafi ya kubuce mana sun kai 250 acikin daren asabar din.

Da misalin karfe 2:00 nd muka ga abin nasu yaki karewa, sai aka fara tunanin tunda suna kara dannowa ne , akace a samu motar da za'a rufe hanyoyin shigowa sai ya zama babu hanya da zasu shigo. Akwai direba na gidan Malam ya dauki mota ya tunkaresu Gaskiya yayi kokari sosai saboda yadda suka tayi masa ruwan wuta kafin yaje , Amma duk da haka sai da ya gitta masu mota. Nan take suka harbe shi yayi shahada.

Sai wani haris ya sake daukar wata motar cikin ta escort din nan ya tafi da ita shima bai dawoba. sun harbeshi. Sai kwamandan harisawa Malam Hamza Yawuri ya dauki motarsa yaje ya kange su saboda suna ta kara dannowa. yana fitowa suka harbeshi.

Ga yunwa ga kishinrwa, sun kuma kara kaimi sosai wajen kashe mutane a cikin daren. Sai aka ajiye mu a kwanar gidan Dakta Mustapha. munyi iya bakin kokarinmu wajen hanasu shigowa. Da asuba aka amshe mu muka je muka yi sallah. Da muka dawo akace ana neman mutum 40 da zasu tsaya a jikin taransufamar gidan Malam wadanda ko me zai faru baza su bar wajen ba.

Ina cikin wadanda aka zaba aka ajiyesu a wajen. Gaskiya sojojin nan sun anfani da iska mai guba, domin kuwa lokacin da suka tunkaro kofar gidan Malam sun yi ta harbin mu , amma cikin ikon Allah ba wanda suka samu. Da suka kasa karasowa inda muke, sai suka harbo mana wata iska mai guba. wani farin hayaki ya turnake wajen. wallahi a cikin mu 40 din nan babu wanda bai fadi kasa ba.

Naji kishirwar da ban taba jiba a rayuwata Naji kasalar da ban taba jiba ba a rayuwata. kawai ruwa nake kokarin in samu. naga wasu suna ta shure-shure, wasu bakinsu na kunfa. Nan na rarrafa na taho wajen wani masallaci dake kusa da gidan Malam, ban samu ruwa anan ba sai wani dan dis na samu a jikin wata buta na jika makogwaro na. Nan sai naji tsananin kishin ya karu.

A nan na gangaro sai na hadu da wasu harisawa da suke daukar mutanen da aka harba a mashin suna fita da su. Da aka ga halin da nake ciki sai aka dauke ni za a fita da ni. Mun tafi kenan, ba mu yi nisa sosai ba, sai kawai naji wata kara, Sai muka fadi. Ashe sojojin sun harbe dan uwan da ya daukoni, Nan take yayi shahada. Ni kuma a wajen na suma. Na farka ne wajen karfe 3:00 nd naga wasu sistoci guda biyu suna yi min fifita.

Ashe ganin halin da nake ciki ne suka shigo dani gida don kar sojojin su karasani. Sunce suma jiya mijinsu yayi shahada. Washegari suka ban naira 1,000 suka ce in shiga mota in koma gida. Da na murmure da La'asar ranar Litinin sai na tashi da nufin in koma gida, amma da yake ban da wani alami a jikina, sai na bi ta kofar gidan Malam don in ga halin da ake ciki. Na ga sun rusa ko'ina, ga kuma gawarwaki nan fululu. Naga yan iskan gari suna ta cire zobba da wayoyi yan uwa da suka rasu. Wani abin takaici da na gani ma idan sun ga riga ko wando jins mai kyau, sai su cire, suna cewa zasu je gida su wanke su rika sanyawa. Ka san a Zaria ba inda ya kai Gyallesu da Tudun wada yan iska.

Har a gida ana cewa ba a gan ni ba, wasu suna cewa nayi shahada Amma kawai sai aka ga na dawo. Na yi ta fama da daukewar nunfashi da na koma gida saboda wannan iskar da suka jefa mana. Na yi ta shan magunguna, abin bai yiba amma cikin hukuncin Allah da yake ina da ruwan Husainiyya, da na rika shan sa, yanzu gashi har na warke, nunfashina ya dawo 'normal'.

ABIN DA YAFI BAN TAUSAYI

Gaskiya abinda yafi ban tausayi, wanda yake sa kullum nake zubar da kwalla shine, irin yadda naga sojoji nan sun nuna rashin imani da tausayi, har yara kanana suke kashewa. Sun rika kasha yara kanana da mata da masu ciki. Don akwai wata da muka dauko ta hanjin cikinta ma a waje yake. Wannan abin yana girgizani a kowane lokaci in na tuna.

ABIN DA YAFI BURGENI

Abinda yafi burgeni shine irin dakewar da 'yan uwa suka nuna. Gashi ba makami garemu ba, amma muka tunkari sojoji masu bindigogi da tankokin yaki. Ni haris ne. amma gaskiya na yaba wa juriyar da dakewar yan Abul Fadlul Abbas. Sun nuna jarumta Fiye da yadda baka zato. Sun bamu hadin kai sosai, munyi aiki tare. Gaskiya irin dakewar da suka nuna ta burgeni. Ita ta kara min karfin guiwa.

SUN YI NUFIN MURKUSHE HARKA NE

Daga bayanin da naji wadandan sojoji nayi. Lallai sunyi nufin murkushe Harka Islamiyya ne, sun so su kashe Malam ne. sun so yaje Abuja ne su kashe shi a can. Cikin hukuncin Allah sai Malam din baije Abuja din ba ya tura Malam Muktar sahabi. Muna Gyallesu ma ya dawo. Wannan abin dama shiryayyene. ko da abin da ya faru a Husainiyya bai faru ba, a wannan ranar sai sun auka wa yan uwa. saidai kuma burin su bai cika ba. Yanzu
wasu sojojin suna ta regret [Da na sanin] aukawa yan uwa da sukayi.

SUN TANBATSA HARKAR NAN ADUNIYA

Ga wanda ke bin abinda ke zuwa yana dawowa a duniya zai kara gaskata abinda su Malam suke fada cewa, duk lokacin suka yi amfani da karfi a kanmu zasu tambatsa harkar ne a duniya. Yanzu Harkar ta zama ta duniya. A wasu wuraren da ba mu san sun san abinda da muke yiba, sai gashi suna fitowa suna zanga-
zangar Allah wadai da ta'addancin da aka yi mana, suna neman asaki Shaik Ibrahim zakzaky da Gaggawa.

SAKONA GA YAN UWA

Lallai wadannan addu'o'in da muke yi akwai nasara, don haka mu kara kaimi da dagewa. Mu zama masu bin tsari da nizami.

Ibrahim Teacher Funtuwa