Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nageria
Litinin

15 Faburairu 2016

06:16:43
735017

An gabatar da maulidin Khatamah a Gombe tare da kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky

'Yan uwa musulmi a garin Gombe sun gabatar da babban taron bukin maulidin Khatamah a jiya Asabar 13 ga watan Fabrairu 2016 tare da kiran #A gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky, da mai dakin sa Malama Zeenatuddeen Ibraheem da sauran dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen tsaro daban daban na kasar

Taron maulidin na Khamatah dai ya sami halartan manyan baki daga sassa daban na cikin garin Gombe da sauran garuruwan dake kusa.

Haka nan kuma a lokacin bukin 'yan makarantar Fudiyyah daban daban sun gabatar da fareti na musamman.

Daga bisani babban bako mai jawabi Malam Adamu Tsoho Jos ya gabatar da jawabi sannan a karshe an mika kyaututtuka ga wadanda suka yi zarra a fannoni daban daban.288