Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Asabar

13 Faburairu 2016

09:57:48
734680

Gangamin goyon bayan 'yan uwa na Bahrain da kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky a Kano

A jiya Jummu'a 12 ga watan Fabrairu 2016 dazun a Kano 'yan uwa al'ummar musulmi suka gabatar da wani gangami na nuna goyon bayan gwagwarmayar al'ummar musulmi a Bahrain, wanda aka saba gabatarwa shekara-shekara a irin wannan watan na Fabrairu. Saidai a wannan shekarar an gwamna gangamin da kiran

#A saki Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Masu gangamin sun rika daga tutocin kasar Bahrain da hotunan masu gwagwarmayar Neman hakki da kuma hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.

Ga wasu hotunan gaggawa da muka dauka a lokacin gangamin da aka gabatar a yau a babban masallacin Fagge dake kano:288