Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Jummaʼa

12 Faburairu 2016

17:14:52
734611

Kagaggun tuhume-tuhume da aka yiwa 'yan uwa Musulmi a kotun Kaduna

A ranar Laraba 10/2/2016 wata Kotun Majistiri ta yi zama a cikin babban gidan yari da ke garin Kaduna a inda aka gabatar da wasu tuhume-tuhume da ake yi wa 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci su 191 wadanda ake tsare da su a gidan yarin bisa zalunci tun sama da wata biyu da suka gabata.

TAKARDAR MANEMA LABARAI KAGAGGUN TUHUME-TUHUMEN DA AKA YI WA 'YAN UWA MUSULMI A KOTU A KADUNA

A ranar Laraba 10/2/2016 wata Kotun Majistiri ta yi zama a cikin babban gidan yari da ke garin Kaduna a inda aka gabatar da wasu tuhume-tuhume da ake yi wa 'yan uwa musulmi na Harkar Musulunci su 191 wadanda ake tsare da su a gidan yarin bisa zalunci tun sama da wata biyu da suka gabata.

Daga cikin tuhumar da Kotun ta yi wa 'yan uwa na Harkar Musuluncin sun hada da: Gudanar da taro ba bisa ka'ida ba, haifar da jikkatar mutane, takurawa al'umma da kuma mallakar makamai (Abubuwa masu fashewa).

Harkar MUsulunci ta yi matukar mamakin irin wannan zama na farko da Kotun ta gudanar a cikin gidan Yari. Ya kamata Kotun ta bayyana wa al'umma dalilinta na gudanar da wannan irin zama nata a cikin gidan Kaso, ko da dai ta kasa yin bayanin dalilin yin hakan. A ce Kotu ta fake da sunan matsalar tsaro ta gudanar da aikinta a cikin gidan Yari ya sabawa ka'idar tabbatar da Adalci, domin kamar yadda ake cewa ne, idan ana so a yi Adalci, to dole a nuna za a yi adalcin.

Don haka muna kallon wannan shari'a a matsayin shari'a ta sirri domin kuwa a doka (Shari'a) ya kamata ne shari'ar da za a yi wa 'yan uwa na Harkar Musuluncin a yi ta a sarari a cikin Kotu ta yadda al'umma za su ji kuma su gani. Abin da ya faru a gidan Yari na Kaduna tamkar boye shari'a ne ta hanyar hana jama'a su ga yadda Kotu ta aiwatar da aikinta. Ko da dai mu babban abin da ya fi damun mu shi ne kazafin da aka yi wa 'yan uwa na Harkar da mallakar makami. Kamar yadda mai gabatar da karar ya bayyana cewa akwai makamai masu yawa da aka samu daga wurin 'yan uwan wadanda akwai bukatar a kai su garin Lagos domin kwarraru su bincike su. Mun yi imani da cewa wannan tuhuma ce ta kazafi aka yi wa Harkar Musulunci a Najeriya (IMN). Yana da kyau mu fahimci cewa da a ce 'yan uwa sun mallaki makamai, to da kuwa wani abu ne kuma na daban zai auku lokacin kisan kiyashin da Sojojin Najeriya suka yi a garin Zariya, don kuwa da an ga dimbin wadanda aka jikkata daga bangaren na Sojoji, wanda kuma ba a ga hakan ba.

Domin a sarari yake duniya ta shaida babu gawar ko da Soja daya da aka gani a yayin wannan harin rashin tausayi da Sojojin Najeriya suka kaddamar a kan fararen hula da ba su dauke da makami a muhallin Husainiyya Bakiyyatullah da kuma gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky. Gaskiyar al'amari dai shi ne bijiro da maganar makami a wannan karo na farko yana nuna cewa mahukunta suna kokari ne ta kowane hali na su samar da wata hujja dangane da auka wa Harkar Musulunci da aka yi. Domin idan ba haka ba me ya sa tun tuni Sojojin ba su bayyana wa al'umma haka ba? Haka kuma, kafin nan ai a mabambantan lokuta sau uku Shugaban rundunar Sojojin Najeriya ta daya da ke garin Kaduna, Manjo-Janar Adeniyi Oyebade, wanda cikin takama ya shelanta cewa shi ya jagoranci wannan Yaki da suka yi, ya kuma bayyana cewa 'yan uwa na Harkar Musuluncin ba su da makamai, sai dai suna da Dankuna, Adda da kuma Sanduna.

Ya kuma kara maimaita wannan zance nasa a yayin wata ganawa da manema labarai a inda Sojojin suka bayyana wa duniya irin nasarorin da suka samu a shekarar 2015.

To, don haka daga wurin wa aka sami makaman da jami'an tsaron 'yan sanda suka kai Lagos domin a bincike su? Tabbas ba dai daga hannun 'yan uwa na Harkar Musulunci ba. Don haka mu na fata al'umma ba za su bari a rude su da wannan karya ba, saboda 'yan uwa na Harkar Musulunci ba su taba ba, kuma ba za su taba daukar makami ko mallakar makami ba. Kuma a tsawon tarihin Harkar nan na kusan Shekaru Arba'in (40) ba mu taba auka wa kowa ba. A kowane lokaci mu ne makiyan mu suke auka mawa, wadanda suke jin tsoron yadda al'umma suke fahimtar wannan kira na Musulunci. Haka nan kuma Jagoranmu Shaikh Zakzaky ya sha fadi cewa " Fada muke yi, ba Fada ba ". Don haka har yanzu muna kara jaddada bukatarmu na a saki Shaikh Zakzaky tare da sauran 'yan uwa musulmi ba tare da wani sharadi ba, don kuwa Allah ne ya yi da sauran kwanansu a gaba, shi ya sa suka tsira daga kisan kiyashin da Sojoji suka yi a garin Zariya a kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA

SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA 08050786093 11/02/2016

Fassara daga Zaharaddeen Sani Malumfashi