Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Laraba

10 Faburairu 2016

17:40:05
734328

An saurari karar 'yan uwa dake tsare a kurkukun Kaduna yau a cikin gidan na kaso

A yau Laraba 10 ga watan Janairu 2016 ne kotu a jihar Kaduna ta fara sauraren karar 'yan uwa musulmi kimanin 200 da gwamnati ke tsare da su a gidan kaso na garin Kaduna, kimanin tsawon wata biyu tun bayan hare haren da sojoji suka kai akan Harkar Musulunci a Nigeria a cikin watan Disamba na bara.

Sai dai a wannan karon a wani abu da ba safai akan yi ba, kotun ta zauna ne a cikin gidan yarin na Kaduna, kuma a ciki ne ta saurari karar. 

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a yau da safe aka jibge jami'an tsaro masu uniform da na farin kaya a kewaye da gidan kason.

Su dai wadan nan 'yan uwa da ake tsare da su an kama su ne akasari daga gidan Malam a Gyallesu lokacin da sojoji suka kai hari a can, kuma wasu daga cikin su suna da raunuka na harbin harsashi a jikin su.

Daga cikin su akwai wasu yara hudu Ibrahim Suleiman, Aliyu Yusuf, Abdullahi Aliyu da Aliyu Ibrahim wadanda shekarun su basu kai 18 ba wanda kotun ta bada belin su.

A gefe guda kuma lauyan 'yan uwa Barista Hussaini Ibrahim ya bayyana damuwar sa ga manema labarai kan yadda aka ajiye wasu daga cikin wadanda yake karewa ba tare da sanin yadda aka kai su kotu ba, da kuma tantance sunan su ba kafin a kai su gidan kason.

Barista Hussain yaci gaba da bayyana a irin wannan yanayin ne zai iya yiwuwa a ajiye mutum na tsawon shekaru aru aru, domin ba shi da wani rubutaccen abu da zai nuna yadda aka tsare shi kuma me ake ciki game da shi. 

An daga sake sauraren karar dai zuwa 29 ga watan na Fabrairu 2016.