Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Talata

9 Faburairu 2016

20:07:45
734217

Muzaharar #A saki Sheikh El-Zakzaky ta Harisawa zalla dazun nan a Gombe

Dazun nan ke nan a yau Talata 9 ga watan Fabrairu 2016 'yan uwa al'ummar musulmi Harisawa zalla a garin Gombe suka gabatar da wata muzahara inda suke kira da #A saki Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Masu muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288