Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Alhamis

4 Faburairu 2016

15:45:05
733380

An yi gangamin kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky da tir da kashe Sheikh Nimr a Amerika

Dimbin al'umma ne a kasar Amerika suka gabatar da wani gangami inda suke nuna rashin amincewar su game da kshe Sheikh Nimr Al-Nimr da kasar Saudiyyah ta yi da kuma yin kira da #A saki Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Masu muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288