Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Laraba

3 Faburairu 2016

14:30:05
733233

An yi muzaharar kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky a Zariya da sauran birane a Nigeria

Dazun nan ke nan a yau Laraba 3 ga watan Fabrairu 2016 'yan uwa al'ummar musulmi matasa a cikin garin Zariya da sauran manyan birane na kasar suka gabatar da wata muzahara inda suke kira da #A saki Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Masu muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

An gabatar da irin wannan muzaharar a garuruwan Sokoto, Kano, Bauchi, Azare, Patiskum, Yola, da sauran birane.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288