Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nageria
Talata

2 Faburairu 2016

10:28:20
733020

An yi gangami mai girma na kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky a New Delhi, India

Dubun dubatan al'ummar musulmi ne suka gabatar da wani gagarumin gangami wanda "Anjumane Haidariya at Karbala Jor bagh -New Delhi India" suka suka gabatar inda suke kira da #A saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

An hada wannan gangamin ne da manufar yin Allah waddai da kisan Sheikh Nimr Al-Nimr a Saudiyyah, nuna goyon baya ga al'ummar Bahrain, al'ummar Yemen da wadanda aka zalunta.

Masu muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288