Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Lahadi

31 Janairu 2016

16:03:16
732768

Fulani 'yan "Kautal Ko' e Julbe" sun yi maulidi tare da kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky

Bangaren Fulani a Harkar Musulunci a Nigeria da aka fi sani da bangaren "Kautal Ko' e Julbe" na garin Gombe sun gabatar da bukin maulidin Manzon Allah[SAWA] tare da yin #A saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban.

Kamar yadda aka sani ne dai Fulani 'yan bangaren Kautal Ko'e Julbe suna gabatar da bukin maulidin fiyayyen halitta na shekara-shekara a Zariya, a wannan karon saboda halin da ake ciki sun gabatar da bukin ne a garin Gombe tare da kiran a gaggauta sakin Malam.Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288