Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Asabar

30 Janairu 2016

15:38:02
732598

Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar, ba zai yi mana adalci ba

A ranar 29/01/2016 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta Nasiru Elrufa’i ta kaddamar da kwamitin bincike dangane da mummunan ta'addancin da Sojojin Najeriya suka yi a kan Harkar Musulunci a cikin watan da ya gabata. Kafin wannan lokacin mun rubuta takardar rashin amintar mu dangane dawannan kwamiti da kuma mambobinsa,

TAKARDAR MANEMA LABARAI: KWAMITIN BINCIKEN DA GWAMNATIN JIHAR KADUNA TA KADDAMAR BA ZAI YI MANA ADALCI BA

A ranar 29/01/2016 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta Nasiru Elrufa’i ta kaddamar da kwamitin bincike dangane da mummunan ta'addancin da Sojojin Najeriya suka yi a kan Harkar Musulunci a cikin watan da ya gabata. Kafin wannan lokacin mun rubuta takardar rashin amintar mu dangane da wannan kwamiti da kuma mambobinsa, amma kuma Gwamnatin Jihar bata kalli wannan koke namu ba. Harkar Musulunci tana kallon wannan kwamitin a matsayin kwamitin 'Tabbatar da laifi', a maimakon kwamitin bincike bisa kwararan hujjojinta kamar haka:

1. Wasu daga cikin Mambobin kwamitin suna da kiyayyar Harkar Musuluncin da kuma mazhabin Shi’a. Don haka a Shari’a ba su cancanci zama cikin ‘yan kwamitin ko masu ruwa da tsaki a cikin kwamitin ba.

2. Gwamnatin Jihar Kaduna ta riga ta nuna rashin adalcin ta tare kuma da nuna matsayarta dangane da Harkar Musuluncin.

3. Sojojin Najeriya da ke cikin kwamitin su ake zargi da mummunan kisan kiyashi, tsarewa bisa zalunci, fyade, konewa da kuma rushe gine-ginen Harkar Musulunci da aka yi.

4. Babu wakilcin Harkar Musulunci a cikin Mambobin kwamitin.

5. Babu Mambobin kungiyoyin rajin kare hakkin bil’adama na kasa ko kasa da kasa a cikin kwamiti.

Bisa wadannan dalilai da muka ambata, adalci, ‘yanci da kuma nuna rashin son kai da ake bukata ga kwamiti a karkashin kashi na 36 a Kundin tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999, da tanajin Hukumar kare hakkin bil’adama ta Afirika A9, da Kundin tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 2004 da kuma Hakkokin bil’adama na duniya abin kokwanton samuwar su ne ga wannan kwamitin.

Don haka gaskiyar al’amarin da ake bukatar samu ba zai samu ba daga wannan kwamitin sakamakon rashin adalcin da aka nuna wanda za a iya ganin sa a sarari ko a kaikaice dangane da wannan al’amari. Saboda idan ana so a yi adalci, to ya zama dole a nuna alamar za a yi adalcin. Saboda haka, har yanzu muna bayyana cewa:

A) Wannan kwamitin da aka kafa bai cika sharuddan Shari’a da kuma hankali ba ta yadda zai iya binciko makasudin abin da ya jaza “Arangamar” da ta faru tsakanin Sojojin Najeriya da ‘ya’yan Harkar Musulunci a Najeriya a ranar 12-14 ga watan Disamba,2015 a garin Zariya saboda rashin adalci da kuma ‘yancin wannan kwamitin.

B) A kafa kwamitin bincike mai zaman kansa wanda zai kunshi mutane masu mutunci da kuma Mambobin kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam na Kasa da Kasa domin gano musabbabin al’amarin da ya faru a ranar 12-14ga watan Disamba,2015 a garin Zariya.

C) A saki Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky daake tsare da shi bisa zalunci, wanda har ya zuwa lokacin hada wannanrubutun ba a ba iyalinsa ko lauyoyi damar ganawa da shi ba a indaake tsare dashi.

SA HANNU

IBRAHIM MUSA

SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA.288