Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Jummaʼa

29 Janairu 2016

18:45:29
732489

Ci gaba da muzaharorin #A saki Sheikh El-Zakzaky a Kano, Gombe, Yola, Bauchi,

A yau Jummu'a 29 ga watan Janairu 2016 ne 'yan uwa al'ummar musulmi a garuruwa daban daban da birane suka gabatar da gangami inda suke kira da #A saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa tare da dukkanin wadanda ake tsare da su a gidajen kaso daban daban

Masu muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kira a gaggauta sakin sa tare da dukkanin wadanda suke tsare.

Tun bayan hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaiwa Harkar Musulunci a Nigeria, da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar a Gyallesu ake ta gabatar da gangami da muzaharori a baki dayan kasar ana kiran a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky.288