Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Lahadi

24 Janairu 2016

10:05:48
731747

An yi muzaharorin kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky a ciki da wajen Nigeria

A ci gaba da raya munasabar tunawa da Arbaeen na shahidan , a jiya asabar an gabatar da muzaharorin ci gaba da kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa ba tare da wani sharadi ba, tare da dukkanin sauran wadanda suke tsare a gidajen kaso daban daban a kasar

An gabatar da wannan muzaharori ne a garuruwa da birane daban daban na Nigeria da kuma Jamhuriyar Nijer.

Mahalarta muzaharar sun rika taken kira da a gaggauta sakin Sheikh El-Zakzaky da sauran dukkanin wadanda suke tsare.

An yi muzaharar a Kaduna, Katsina, Kano, Gombe, Sakwwato, Bauchi, Yola, Suleja, Azare, Potiskum, birnin Maradi a Jamhuriyar Nijer da sauran birane.288