Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Talata

19 Janairu 2016

16:55:47
731179

Dalibai sun gabatar da ggarumin gangamin #A saki Sheikh El-Zakzaky a Abuja

A yau talata 19 ga watan Janairu 2016 ne dalibai daga bangarori daban daban na kasar karkashin lemar "Students and National Youth Service Corps members" suka gabatar da gagarumin gangamin kiran a saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da sauran dukkanin 'yan uwa dake tsare.

An gabatar da wannan gangamin ne a yau a Abuja gaban ofishin hukumar kula da hakkin dan adam ta kasa.

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Mahalarta wannan gangami sun daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna kiran a gaggauta sakin sa, sannan kuma sun rika daga kyallaye da rubutun tir da hare-haren sojoji a Zariya.