Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Talata

19 Janairu 2016

10:23:03
731127

Malam Sunusi Abdulkadi yayi hira da manema labarai kan yunkurin rusa Markaz

Da misalin karfe 11nr a ranar Litinin 18 ga watan Janairu, 2016 'yan Uwa almajiran Shaikh Ibraheem El Zakzaky (H) na Kano Karkashin jagorancin Malam Sunusi AbdulKadir suka gabatar da taron manema labarai dangane da yunkurin wasu na haddasa fitina a jahar Kano. An gabatar da Wannan taron ne

Da misalin karfe 11nr a ranar Litinin 18 ga watan Janairu, 2016 'yan Uwa almajiran Shaikh Ibraheem El Zakzaky (H) na Kano Karkashin jagorancin Malam Sunusi AbdulKadir suka gabatar da taron manema labarai dangane da yunkurin wasu na haddasa fitina a jahar Kano.

An gabatar da Wannan taron ne domin cin karo da wata takarda da aka aika wa Gwamnan Kano mai dauke da sa hannu Alh Lawan Hasan mazaunin Kofar-Waika na 12 ga Junairu, 2016 yana mai ambaton wadansu korafe-korafen wasu da kuma matakin da suke son gwamnatin Kano ta dauka da ya kunshi rushewa ko kwace cibiyan Yan uwa na Kano (Markaz).

Kadan daga Kafafen Yada labaran da suka samu halartan taron aka kuma basu takardan manema labaran sun hada da Express Radio, Rai Power Radio, Radio Tehran, Leadership Newspaper, Almizan, Tha Nation Newspaper.

Wakilan kafafen watsa labaran kuma an zagaya da su Markaz din na Yan uwa kuma sun gani. Malam Sunusi AbdulKadir yayin amsa tambayoyin watsa labarin ya nuna irin mamakin sa ga wannan takarda da aka ci karo da su bayan abinda aka sani daga mazauna unguwa shine kakkyawan alaka da ke tsakanin jagoran ‘Yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky (H) na Kano Shaikh Muhammad Turi suna masu yaba masa wajen jibintan al’amuran al’umma da kuma kokarin hadin kai na fiye da shekaru sha uku da yake zaune a Kofar-waika.

Malamin ya kara jaddada wannan tarbiyan da mazaunan unguwar suka gani a wajen Shaikh Turi akansa ake, kuma za a kara riko da shi, ya kuma jaddada duk da yake wasu na son haddasa rikici gwamnatin Kano za ta cigaba da riko da kaucewa dukkan dasisa da kikisinar wasu na ganin an haddasa rikici. Malamin ya kara kira da ‘Yan unguwa da kada su biye wa masu yada jita- jita ko kokarin haddasa rikici, kofa kuma a bude take wajen tuntuba ga duk abinda suke son kara fahimata tare da hadin kai. Da aka tambayi ko ‘Yan uwa na da wani mataki da za su dauka, Malamin ya ambaci, matakn da ake dauka a baiyane suke da kokarin isar da gaskiyar al’amari ga dukkanin bangarori, da kuma Karin fahimatar juna.288