Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Litinin

18 Janairu 2016

07:20:40
730988

Sharuddan halartan mu gaban kwamitin bincike da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike kamar yadda ta yi alkawari. Ko da dai Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ta yi kira ne da a kafa amintaccen kwamiti mai zaman kansa wanda zai kunshi mutane masu mutunci da kuma ‘yan rajin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa domin gano makasudin yin kisan kiyashi a

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike kamar yadda ta yi alkawari. Ko da dai Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ta yi kira ne da a kafa amintaccen kwamiti mai zaman kansa wanda zai kunshi mutane masu mutunci da kuma ‘yan rajin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa domin gano makasudin yin kisan kiyashi a garin Zariya da kuma abin da ya biyo bayan kisan. Sanannen al’amari ne abin da ya faru a ranar 12 ga watan Disamba, 2015 wanda ya sababba yi wa ’yan uwa na Harkar Musulunci Kisan kiyashi, jikkata daruruwa, garkame wasu a gidan yari da kuma lalata kaddarorin Harkar Musuluncin. Kuma wani shiryayyen al’amari ne na take hakkin Dan Adam wanda Gwamnatin tarayya tare da hadin guiwar Gwamnatin jihar Kaduna suka tsara kuma suka aiwatar.

Harkar Musulunci ta yi amannar cewar al’amarin da ya sabbaba kafa kwamitin tsararren al’amari ne, haka kuma za ta kasance a gaban Kwamitin ne bisa sharudda kamar haka:

A saki jagoran Harkar Musuluncin ba tare da wani sharadi ba. Domin kuwa Gwamnati tana tsare da shi ne kasantuwar ta san shi ne taskar Harkar Musuncin wanda zai tsara tare da bayar da umarnin yadda za a tattara bayanai da kuma gabatar da hujjoji. Jami’an tsaron soja da ‘yan sanda su bayyana dukkanin ‘yan uwan da suke tsare da su tare kuma da ba lauyoyin Harkar Musuluncin damar ganawa da su. Domin kuwa Harkar Musulunci tana da kwakkwarar shaidar cewa akwai dimbin ‘yan uwa na Harkar da ake tsare da su a barikokin soja da kuma sauran wuraren tsare mutane.

Jami’an tsaron Sojojin Najeriya da kuma ‘yan sanda ya zama dole su bayyana adadin ‘yan uwan da suka kai Asibitoci da kuma wuraren da Asibitocin suke domin ba lauyoyin Harkar Musulunci damar tattaunawa da su don fuskantar wannan kwamiti.

Dole ne Kwamitin ya tabbatar da ba da kariya ga Mambobin Harkar Musuluncin da za su bayyana a gaban Kwamitin domin gabatar da hujjoji.

Gwamnatin jihar Kaduna da kuma Rundunar ‘yan sanda ta Kaduna su bayyana adadin mutanen da suka kai kotu da kuma wadanda suke tsare a gidan Yari. Wannan ya zama tilas domin kuwa rundunar ‘yan sanda ta Kaduna da Gwamnatin jihar Kaduna a asirce, kuma ba bisa doka ba sun ba da umurnin garkame ‘yan uwa masu dimbin yawa a babban gidan yari na Kaduna ba tare da gurfanar da su a gaban shari’a ba. Domin kuwa a halin yanzu akwai ‘yan uwa sama da dari biyu (200) da ake tsare da su a babban gidan yarin da ke Kaduna.

Harkar Musulunci a Najeriya tana da kididdigar adadin ‘yan uwa guda 730 wadanda ko dai sojoji sun kashe su ko kuma sojoji suna tsare da su a hannunsu, a yayin da kuma sojojin suke ikirarin cewa babu wani ko da mutum daya cikin ‘yan uwa na Harkar a hannunsu. Don haka a saki wadanda sojoji suke tsare da su, a kuma mika gawarwakin wadanda aka kashe domin yi masu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Muna sane da cewa akwai wasu membobin Kwamitin da su ba yan ba-ruwanmu ba ne a kan wannan batu, kuma ba wadanda za a iya dogaro da su kan samun adalci ba ne, saboda yadda suka fito balo-balo suna nuna kiyayyarsu da Harkar Musulunci da jagorancinta ta hanyar maganganunsu, rubuce-rubucensu da ayyukansu a baya. Wasunsu ma har kira suka yi ga gwamnati da ta murkushe Harkar Musulunci ne a baya. IMN ba ta tsammanin samun adalci daga wadannan mutane saboda matsayar da aka san su da ita kan Harkar Musulunci da kuma mazhabin Shia. Irin bakar gabar da suka nuna ga Harkar Musulunci ta sa dole sun kassara tunaninsamun wani adalci a tattare da su kan wannan batu. Maimakon su ma da 'yan rajin kare hakkin bil'adama aka sa a cikin Kwamitin.

Sai Gwamnatin jihar Kaduna ta cika wadannan sharudda da muka ambata, idan tana so ta gamsar da Harkar Musulunci. Kasancewar Gwamnatin jihar tana da sa hannu a cikin wannan laifi tun da ta lalata mana kaddarori da kuma kawar da hakikanin shaidun da za su tabbatar da irin ta’asar da sojoji suka yi wa Harkar Musulunci, ba a kafa wannan kwamitin ba ta yadda zai iya zakulo rashin adalcin da Gwamnatin tarayya da kuma Gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa Harkar Musulunci ba.

SA HANNU:

IBRAHIM MUSA
SHUGABAN MEDIA FORUM NA HARKAR MUSULUNCI A NAJERIYA
08050786093
17/01/2016