Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : harkarmusulunci a nigeria
Lahadi

17 Janairu 2016

19:27:36
730965

Abin da aka yi mana ya fi karfin zalunci - Hirar Malam Yakubu Yahya Katsina da Almizan

A farkon wannan makon ne tawagar Editocinmu ta yi takakkiya zuwa Katsina don ganawar musamman da Shaikh Yakubu Yahya a kan harin da sojoji suka kai wa ’yan uwa da kuma kama Jagoran Harka Islamiyya da gwamnati ta yi. A cikin tattaunawar, wacce ta tabo janibobi daban-daban, ya warware zare da abawa a

 A farkon wannan makon ne tawagar Editocinmu ta yi takakkiya zuwa Katsina don ganawar musamman da Shaikh Yakubu Yahya a kan harin da sojoji suka kai wa ’yan uwa da kuma kama Jagoran Harka Islamiyya da gwamnati ta yi. A cikin tattaunawar, wacce ta tabo janibobi daban-daban, ya warware zare da abawa a kan abubuwan da suka faru, tare da bayyana abin da ake so gwamnati ta yi. Sai wanda ya zauna tsaf ya karanta ne kawai zai riski abubuwan da ke ciki.

ALMIZAN: Ko Malam zai yi mana tilawar abubuwan da suka faru a Zariya a ranar 12/12/2015 a gurguje?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Abin da ya faru da mu a ranar Asabar 12/12/2015 daidai 1 ga Rabi’ul Awwal 1437 din nan abu ne wanda yake na bakin ciki. Na’am, muna zaton sa kowane lokaci, tunda ita jarabawa daga Allah (T) takan zo wa bawa, sai dai ba ka san wane lokaci, ko kuma da wace irin siga za ta zo ba. Amma wannan wadda ta zo, ta ba mu mamaki kwarai da gaske. Galiban wasu abubuwan kafin su zo mukan samu labari, sai ka ga sun wargaje. Su Malam sukan ankarar da mu cewa, an shirya kaza da kaza. Kuma daga baya sai abin ya wargaje. Amma wannan, kawai sai muka wayi gari ga sojoji sun zo bakin Husainiyya Bakiyyatullah, inda nan ce Cibiyarmu ta gudanar da al’amuranmu na addini.

Lokacin da ’yan uwa ke shirye-shiryen yamma ta yi Malam ya zo a cire tuta ta juyayi a sa ta farin ciki, wacce ke almanta cewa an fara Maulidi, tun farko-farkon rana, wajen 11-12:00nr haka, sai ga sojoji sun zo da bindigogi da akwatunan harsasai suna kallon ita Husainiyya din. A lokaci guda kuma can kasa wajen PZ sun ajiye wasu mutanensu, sannan wajen Kwangila ma sun ajiye wasu. Wato alamar ke nan wanda zai taho daga cikin Zariya ya bi wannan hanya ta Sokoto Road an datse shi, wadanda za su taho daga Kano, Funtuwa da sauran wurare su ma an datse hanyar.

Na’am ’yan uwa sun fito sun yi magana da sojojin don jin dalilinsu na zuwa. ’Yan uwa sun je sun same su cewa mun ga kun zo kun yi sansani a nan gidan man wanda ke kallon Husaniyya, wanda kuma a bara wani abu mai kama da irin wannan ya faru, an kashe mana mutane wajen guda bakwai. Ga harin da suka kai mana ranar Kudus, ranar Asabar kuma suka zo Husainiyya suka harbe mana mutane. Suka ce saboda tsoron sake faruwar irin haka, da dai za ku koma gaba, ko kuma ku yi baya, saboda nan yau muna da taro. Ana cikin wannan tattaunawa ta hankali, sai wasu mutane da suke cikin wata mota suka zo suna maganganu marasa dadi, suna iface-iface, suna wasa wuka a kan titi. Muna ganin wadannan mutanensu ne. Sai wasu cikin sojoji suka fara harbi.

Ba a jima da wannan ba, kuma sai ga shi Shugaban sojoji da aka ce zai je ya gai da Sarkin Zazzau da kuma bikin yaye kuratan soja ya taho. A nan ma ba a jima ba sai aka bude wuta. Kamar yadda muka samu labari daga wajen ’yan uwan da ke wajen a lokacin da ake tattaunawar, akwai wata mota da ke biye da shi Shugaban sojojin, wani Janar jar fata ya sauko, zai iya zama Balarabe ne, zai iya zama Bature, zai iya zama Bayahude, amma dai jar fata ne, kuma Janar ne, kuma ba shi kadai ne a cikin motar ba. Bilhasali ma shi ya fara ba da umurni a bude wa ’yan uwa wuta. Kafin nan sai da suka raba mutanensu. Yaki sosai. Kamar mutum ya kwanta yana neman ya harbi mutane.

Daga baya sai suka sanar a rediyo cewa Shugaban sojoji ya tsallake rijiya da baya, bayan ’yan Shi’a sun yi yunkurin kashe shi. Wannan ya ba mu mamaki ba kadan ba. Saboda gaskiyar Magana, wani abu mai kama da haka bai taba faruwa ba. Wannan hanya, hanya ce da kowa ke bi ya wuce. Ita ce babbar hanyar shiga Zariya. Sannan kuma akwai barikin sojoji a kusa da wajen, kuma suna zirga-zirga ko da kuwa muna gudanar da ‘program’ dinmu ne. Domin muna da tsarin kula da ababen hawa. Akwai ’yan uwan da ke kula da ‘traffic’, sojoji sukan zo su wuce, ba wani abu da ya taba faruwa. Amma a wannan karon abin da suka shirya ke nan.

Mun dauka wannan abin da ya faru tsautsayi ne, ba wai an shirya shi ba ne. Domin bayan harbe-harben da suka yi, sai komai ya lafa, sai kuma muka ga sun sake dawowa sun ci gaba da bude wuta. Kuma cikin dare, sai kuma muka ji sun fara habe-harbe a Gyallesu. Kun ga ya tabbatar mana da abin da muka zata ke nan, na cewa wani shiri ne da aka yi. Wannan abin da ya faru a Husainiyya masomi ne, tsokana ce. Ya kamata ya zama abin da suka yi a nan ya wuce, tunda sun bude hanya sun wuce. Sai kuma a kama wadanda ake zargi a kai su kotu.

Sai daga baya muka fahimci wadannan awowin da suka yi suna jiran umurni ne da kuma hada wayoyin hanyoyin da za su bi don aiwatar da shirin nasu. Shi ne suka fara. Akwai mamaki abin da ya faru a Husainiyya. Tsakanin Husainiyya da Gyallesu ba zai kasa kilomita biyu ba, sai kuma ya zama an bi mutane can, an yi masu abin da aka yi a can.

ALMIZAN: A farko sun ce sun dauki matakin da suka dauka ne saboda an yi yunkurin kashe Shugabansu, suka dawo suka ce an tsare masa hanya ne, yanzu kuma suna nuna wani ‘video clip’ da ke nuna Harisawa na fareti. Me ya sa kake jin suke ta caccanza dalilai?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Dama wannan matakin da suka dauka ajiyayye ne. Alal misali mutumin da ya ce an tare wa Shugabansa hanya, kuma an bude hanya an wuce, kuma daga baya sai suka dawo suka ce ana tsare wa mutanen Zariya hanya ne. Ka ga cikin maganganun biyu wacce za mu dauka? Tun farko maganganun sun fara karo. Sannan kuma tafiyarsu Gyallesu da kai hari can, ya sake karyata wannan zargin. Me ya kai su can kuma? A can an tsare masu hanya ne, ko kuwa Shugaban sojoji ya bi ta nan ne? Cikin maganganun guda uku ba na kamawa. Kawai shiri ne wanda aka shirya, kuma aka aiwatar da shi.

ALMIZAN: Bayan abubuwan da suka faru na kashe-kashe da rushe-rushe, an kama Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, kuma tun lokacin da aka kama shi, mun ji an ce har yanzu ba a bar wani daga cikin iyali, ko danginsa sun gan shi ba.

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Lallai wannan mu ma ya daure mana kai matuka, kuma yana ba mu mamaki. Wannan ya karya dukkan dokoki na kasashen duniya baki daya. Ya karya dokar ita wannan kasar. A doka in an kama mutum ana tuhumar sa da aikata wani laifi a cikin awa 24 za a kai shi kotu, a sanar da shi laifin da ake zargin ya aikata. In na saki ne, ko na beli ne, ko kuma na kai wa gidan yari ne, sai a yi. Amma ba a yi wa Malam haka ba. Wannan ya karya dokokin duniya, wanda babu yadda za a yi soja mai makami ya harbi wanda bai da makami irin nasa.

Dokokin duniya sun haramta soja ya harbi wani mutum wanda bai dauke da makami, ko da yana da sanda ne ko wuka. Domin ba a kallon su a matsayin makamai. A wannan zamanin, makami shi ne bindiga. Don haka idan soja ya harbi wanda bai da bindiga, wannan karya doka ne ta kasa da kasa. Shi kuwa harba gurneti sai a wajen yaki. Sannan sun karya ita kanta dimokuradiyya din. Domin ita dimokuradiyya ta ginu ne a kan cewa mutane na da ’yancin fadin albarkacin baki, ko ’yancin tarurruka, ko ’yancin addini, ko ’yancin yin taro cikin lumana. Amma su sun karya duk wadannan dokokin. Don haka dan sauran mutuncin da ake kallon Nijeriya da shi a sauran kasashen duniya ya zube. Saboda duk wasu dokokin duniya na kasa da na aikin soja ma sun karya. Ka ga wannan ya nuna maka wannan shiryayyen abu ne da ake so a aiwatar da shi ko ta halin kaka.

Sannan kuma wannan bidiyon da suka saki, wanda wannan ke nuna cewa su ’yan uwa ne suka fara tsokanarsu, su ma’abota hankali da kwararrun ’yan jaridu da na ji suna tattaunawa a kansa, suna cewa lallai wannan bidiyon an yi wasa da shi. Akwai abubuwan da aka kara da kuma abubuwan da aka rage. A bidiyon da ’yan uwa suka dauka wanda ke nuna hakikanin abin da ya faru, an fara sakinsa, kuma yana karyata wancan.

Sannan kuma yanzu na ga suna nuna bidiyo na fareti na Harisawa, shi ma ka ga wannan wata katuwar karya ce. Na’am, Harisawanmu suna da kaya na nizami na motsa jiki. Abin da kowa ya sani shi ne, Harisawanmu masu taimakon kai-da-kai ne. Don aikinsu taimaka wa juna. Na farko tsara tarurruka. Na biyu taimakon jama’a, kamar share kwatoci, kawar da shara, kashe gobara da duk wani abu wanda zai taimaki jama’a, shi ne aikinsu. A lokacin bukukuwa kuma suna saka wadannan kayayyakin domin su kayatar da taro. Sannan kuma ba mu kadai muke yin wannan ba, kungiyar Izala, Darika da Kiristoci suna da wannan. Duk duniya an san su, kuma ba su taba zama matsala ba. Ka ga mu sun dauki namu a matsayin matsala suna farfaganda da shi. Bayan sun yi mana ta’addanci, sai kuma suka biyo da farfaganda.

Babban makasudin wannan shi ne a bata mana suna, a raba mu da jama’a, a shiga tsakanin mu da al’umma. Bayan kuwa al’ummar nan ta ga irin zaluncin da aka yi mana, kuma sun tausaya mana matuka, illa wadanda da ma bakinsu daya. Akwai wadanda bakinsu daya da azzaluman da suka zalunce mu, wadansu ma Malamai ne da sunan addini suna goya masu baya. Ba mu yi mamaki ba, domin su dama irin wadannan an tanade su ne don irin wannan ranar, su yi irin wannan aikin. Ban da su duk al’umma masu neman adalci, Musulmi da Kirista, sun tausaya mana a kan abin da aka yi mana.

Gaskiyar magana abin da aka yi mana ya wuce zalunci. Domin ana zaluntar mai rai ne, to mu har gawawwakinmu ba a kyale ba, har makabarta an bi mu. An je an hake makabartun Shahidai a Darur Rahama, an rusa gine-ginen wurin. An je kuma gidan da kabarin Mahaifiyar Malam yake, an rushe ginin, an lalata wajen. Duk da cewa akwai ka’idar da doka ta tanada idan ka yi gini ba daidai ba, akwai Hukumar da ake kira KASUPDA idan a jihar Kaduna ne, wacce ke zuwa ta ba ka takarda cewa ka je ka amsa kira ka yi bayani a tattauna, idan ka yi jinkiri, ko ka yi taurin kai, sai ta zo ta ba ka ‘notice’ kowa ya gani. Sannan bayan haka a kai ka kotu, ko kuma a dauki matakin shari’a a kanka, bayan an shafa maka jan fenti. Amma duk ba wanda aka yi mana. Nan take kawai aka rusa gine-ginen gaba daya. Idan sun ce Husainiyya an gina a bakin hanya, ko kuma an yi ba bisa ka’ida ba, to ita kuma makabarta fa? Kamar gidan da kabarin Mahaifiyar Malam yake, gidan gado ne. Ba wai maganar Malam ya saya a wajen wani ba ne. Ita ma kuma Darur Rahama wuri ne da aka gado. Tun ba gwamnati wajen yake. Tun Bature bai zo ba mutane suka mallaki wajen. Ka ga da wata manufa ne kawai aka yi.

ALMIZAN: Wasu suna cewa duk an dauki wadannan matakan ne da nufin a tunzura ’yan uwa su dauki doka a hannunsu.

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Haka ne. Akwai wannan ma. Yau kamar shekara 25. Mun dawo daga Kano dare ya yi mana sosai, a lokacin Kwamishinan ’yan sanda Ali Jos ne, daidai shigowa gari, sai aka kama mu aka kai mu Police Statian. Sai Area Commander na wajen ya kira ni ofishinsa a cikin daren mu tattauna da shi. Ya yi min tambayoyi masu yawa a kan ma’anar Harka da kuma inda aka sanya gaba. Bayan duk na gama yi masa bayani, sai ya ce; “Bari in fada maka gaskiya Malam, abin da gwamnati ke so shi ne ku dauki makami. Amma kuma kun ki”. Ya ce da kun dauki makamai, da mai zama ya zauna, matafiyi ya tafi. Ya ce; “Wannan shi ne abin da gwamnati ke bukata”. Sai na ce, ai mu ba mu da wannan shirin. Kuma ba za mu yi shi ba.

Sai kuma bayan faruwar wannan ta’addancin da sojojin suka yi mana, wani babban jami’in tsaro ya zo yi mana jajen abin da ya faru. Bayan ya ji duk ra’ayoyinmu da kuma inda muka sanya gaba. Sai yake cewa; “Gaskiya Malam abin da ake bukata shi ne ku dauki makami, wanda zai sa a samu damar daukar matakin da ake so”. Sai na gaya masa cewa yau shekara 25 ke nan wani jami’in tsaro ma ya fada min haka.

Ka ga wannan sun yi kuskure. Domin ba hadafinmu ke nan. Ba bindiga ce ta tara mu ba. Duk yawanmu ba bindiga aka sa muka zo ba, kuma ba za ta tarwatsa mu ba. Malam (H) ya sha fada cewa da buhunan makamai da na wuwwi daya ne a wajenmu. Ba mu da bukatar makami a da’awar da muke yi. Fada muke yi, ba fada ba.

Ai duk abin da suke yi mana, hatta hana ganin Malam da rike shi da suka yi ba labarinsa duk suna so ne mu tunzura mu yi wani abu. Alhali ita Harkar nan tana da nizami, tana da tsarin da aka dora ta a kai, kauce wa wannan tsarin cin amanar Malam ne da kuma tsarin da ya dora Harkar a kai. Abin da ake bukata ita al’umma ta waye ta fahimci addininta, ta ce shi take so. Shi ke nan. Ita da kanta ta yanke wa kanta hukunci. Amma maganar a dauki makamai a yi fada ba ya cikin tsarin wannan Harka din. Idan ka ga wani da makami a cikinmu, to turo shi aka yi, ba namu ba ne. Idan mun kama shi ma, za mu mika shi ne ga wadanda suka turo shi.

ALMIZAN: An ruwaito Malam yana cewa za ku tafi kotun duniya…?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Ai yanayi shi ke haifar da komai. Tunda ba su jin kira na kunne na su yi adalci, ba su jin duk wani abu wanda ake masu, dokokin kasar ma ba su dauke su a bakin komai ba. Akwai wasu dokoki da aka tanada idan mutum ya matsu, kuma ba a yi masa adalci ba, yana iya kai kara. Muna da mahanga ta namu bangaren, Malamanmu na Fikihu sun karantar da mu cewa, bai halatta mutum ya kai kara inda bai dace ba, amma in an matsa masa, ya zama ba shi da wata mafita, ya halatta a gare shi ya kai karar inda za a bi masa hakkinsa. Tunda muna da wannan mahangar a addini, to za mu kai kararmu tun daga karamar kotu har zuwa ta duniya.

ALMIZAN: A duniya ana ta nuna jimami na wannan abin da aka yi, ana ta Muzaharori da gangami. Amma abin mamaki a nan kasar sai wasu Malamai suke nuna goyon bayan abin da aka yi. Kun yi mamaki da haka?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Bai ba mu mamaki ba, amma ta wani janibi ya ba mu mamaki. Abin da ya sa bai ba mu mamaki ba, Malam, Allah ya kara kare shi, ba shi kadai ne mai neman a aiwatar da adalci a duniya ba, shi wani bangare ne na wannan gungu na al’umma masu neman a shimfida adalci ga kowa a doron kasa. Saboda haka wadannan sautuka da suka hada sautukansu da namu, ganin cewa sai an saki su Malam, irin wadannan sautukan ne masu neman adalci da suka san daidai, kuma suke ganin abin da aka yi ba daidai ba ne, saboda haka ya kamata a bi hakki. Saboda haka ba mu yi mamakin su wadannan sautukan ba. Kowane bangare akwai masu son adalci da gaskiya. Za ga ka wasu Muzaharorin da ake yi a sauran kasashen duniya ba Musulmi ba ne, amma da yake sun san hakkin dan Adam, wannan ‘humanty’ din, ko ’yan’adamtaka shi ne ya motsa mutane suka fito suke neman sai an yi adalci.

A nan cikin gida kuma akwai wasu mutane da ake ce wa Malamai da suka fito suna murna, wasu ma har da walima, wadannan dama kayan aikin azzaluman da suka auka mana ne. Dama an tanade su ne domin irin wannan ranar da irin wannan lokacin. Da jimawa aka yi haka. An kafa masu gidajen talabijin da rediyo, ana ba su kudade don yin wannan aikin ta bayan gida.

Tabbas wannan shirin na auka wa Harka Islamiyya shiri ne na Amurka da Isra’ila, kuma suna da Wakilansu a cikin kasashen Larabawa. Akwai wata kasar Larabawa kakkarfa, wacce take dasawa da Amurka da Isra’ila, kuma ta hanyar wannan kasar ne, su wadannan mutanen da suke kiran kansu Malamai ke samun kudade da goyon baya don yin aikin da ake so su yi. Saboda haka abin da Amurka da Isra’ila ke son yi, wanda ya shafi Musulunci da Musulmi, ta hanyar wannan kasar ake zartar da shi. Ita kuma sai ta bai wa yaranta. Kuma kowa ya sani cewa Malaman nan yaranta ne. Sai su shiga gidajen rediyo da talabiji da masallatan da aka samar masu don yin wannan aikin su isar.

Dama wata biyu kafin faruwar wannan waki’ar sun yi ta bi lungu-lungu, sako-sako, unguwa-unguwa, suna wa’azin kafirta mu. Saboda sun san me aka shirya, kawai suna jiran lokaci ne. Kuma kowa ya gani gidan talabijin na Saudiyya da ake kira Al-Wasal, wata biyu da suka wuce ya yi wani sharhi na musamman da ke nuna damuwa kan yaduwar mazhabin Ahlul Baiti ta hanyar kiran da Malam ke yi a kasar nan. Suka ce wannan abin takaicin sai an dauki mataki mai tsauri a kansa don dakatar da shi. To, ka ga yanzu suna ganin bukatarsu ta biya, shi ya sa suke walima da murna. Amma ban da su, sauran al’ummar Musulmi suna bakin cikin abin da ya faru da mu ne. Irin ta’aziyyoyi, jaje, buga waya da zuwa da kai da muke samu ya nuna haka. Kuma tarukan da muke yi ma sun tabbatar da haka, yadda ake bumbuntowa ana zuwa. Ka ga al’ummar tana tare da mu. Kawai wasu ’yan tsirarun mutane da aka saye su aka biya, sune ke aikin da aka sanya su.

ALMIZAN: Wadannan Muzaharori da gangami da ake yi a kasashe daban-daban na duniya suna tasiri kuwa?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Sosai kuwa suna tasiri. Ai ita Muzahara kamar wani makami ne da ke canza abubuwa a wannan zamanin. In ban da Shugabannin kasar nan doka ba ta aiki a kansu, kuma ba su san kimar talakawa ba, ai in wasu kasashen ne, wadannan Muzaharorin sun isa su canza abubuwa da yawa. In wasu kasashen ne aka yi Muzaharar ranar daya, za su canza abubuwa. Har Minista da Shugaban kasa sai su sauka. Ko kuma an yi niyyar yin wani abu sai kawai a fasa in mutune suka fito suka ce ba su so. Kamar a Indiya gwamnatin kasar ta ce za ta yi wani katafaren aiki a wasu gonaki na talakawa. Da suka yi Muzahara, sai gwamnatin ta fasa aikin. Kuma a Habasha sati biyu ko uku da suka wuce, su ma akwai wasu gonaki da aka karbe na talakawa za a gina unguwar masana’antu; da talakawa suka yi bore, sai gwamnati ta dakatar da aikin don a sasanta da mutane. Saboda haka Muzahara tana da tasiri. Amma wadannan mutane da yake ba su san kimar wadanda suka zabe su ba ne, da bazar talakawa suke rawa, amma in sun hau kan mulki, to ba su kallon talakawan, ba su ma san akwai su ba. Shi ya sa a nan ake ganin kamar ba a ganin tasirin abin. Amma a kasashen waje Muzaharori suna tasiri. Kuma a nan din ma suna yi.

Domin abin da muka fahimta shirin su, bayan sun kai hari a Zariya, za su bi dukkan inda ’yan uwa suke ne su yi. Tir din da sauran kasashen duniya suka yi, da kuma Muzaharorin da aka kwana ana yi a daren Asabar, aka wayi gari Lahadi ana yi, ya sanya sun ja numfashi. Tarukan da suka yi na Gwamnoni sun nuna cewa sun fahimci abin da ake nufi shi ne a tarwatsa kasar nan, musamman ma yankin nan na Arewa. Wannan ya sanya sun dan sassauta wa al’amarin. Amma lallai suna tasiri, domin suna gani suna ji, don ko’ina akwai Wakilansu.

ALMIZAN: An kafa kwamitoci na binciken abin da ya faru, ya kuke kallon wadannan kwamitocin?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Mun riga mun yi bayanai a kan haka. Ba yadda za a yi Area Commander ya binciki Manjo-Janar? Area Commander, wanda ke fatan ya zama Kwamishina, ya zama AIG, sannan ya zama IG, a ce kuma shi ne zai binciki Laftanar-Janar? Kai ka san ba zai yiwu ba. Wannan wasa ne kawai. Don haka ba mu gamsu da shi ba.

Kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa, shi ma lallai ba mu gamsu da shi ba, tunda shi Kwamiti ana yin sa ne daga bangarorin da abin ya shafa. Babu wanda ya kawo mana takardar gayyata. Ba wanda ya ce ina muke, ya ake ciki, ballantana a ji ta bakinmu. Kuma shi Gwamnan ya yi jawabi, ya riga ya yanke hukunci, ya dora mana laifi tun kafin kwamitin ya zauna ya yanke hukunci. Inda yake tuhumar an gina ba bisa ka’ida ba ya zartar da hukuncin sa kawai ya rushe.

Hatta shi kansa Buharin na yi mamakin abin da na ji ya fada, duk da yake ya kafa kwamiti, kuma ya ce ba zai ce komai a kan lamarin ba, shi kansa ya yanke hukunci. A wannan hirar da ’yan jarida suka yi a talabijin ranar Laraba da ake kira Media Chat, ya ce an ba shi labarin mutanen nan suna tare hanya. Ya aka yi ya sane? Kuma wai an doki kirjin Janarorinsa. An kafa gwamnatin cikin gwamnati. Ta ina ya gani? Kuma ya aka yi ya sani? Kwamitin da ya kafa ne ya mika masa rahoto? Ba ya ce ba zai ce komai ba sai bayan kwamitin da aka kafa ya mika rahoto?

Na yi mamaki da na ji yana cewa wai an kafa gwamnati cikin gwamnati. Wannan shaci-fadi ne kawai. An san yadda ake kafa gwamnati, ko dai a kwata da makami, ko kuma a ajiye akwati a jefa kuri’a. A wannan zamanin dai a wannan nahiyar tamu, ta wadannan hanyoyin ake kafa gwamnati. Yaushe ne muka fafata da makamai muka amshi gwamnati? A ina aka ajiye akwati aka jefa mana kuri’a muka zama Shugabanni? A ina hedikwatar take? Su waye Shugabannin? Ina Ministoci, Gwamnoni da Kwamishinoni?

Kuma in muka dawo ta bangaren addini, tunda kasar nan ta mutanen da suke da’awar addini ne, akwai Kirista da Musulmi. Musulmi da Kirista duk sun san cewa duniyar nan kayan Allah ce, kasar, rana, wata da taurari, komai kayan Allah ne, duk wani mai addini ya sallama wa Allah a kan wannan. Ya aiko Annabawa da littattafai yadda za a tafiyar da rayuwa a doron kasa, to ga tambaya. Shi me da’awar an kafa gwamnati cikin gwamnatinsa, to shi kuma da ya kafa gwamnati cikin gwamnatin Allah fa? Ko kuwa shi gwamnatinsa ta Allah ce? Ko kuwa abin da Allah ya saukar ne yake gudanarwa a cikin kasar Allah a madadin Allah Ta’ala a Musulunce, ko a Kiristance? Me ya sa Allah ya kyale shi, ya sanya masa ido yake tafiyar da gwamnatinsa a cikin gwamnatin Allah? Me ya sa zai tuhumi wasu da cewa sun kafa gwamnati cikin gwamnatinsa? Balle ma kawai shaci-fadi ne. Zance ne kawai na farfaganda da kokarin bata suna.

Kuma ya kamata ya zama kwamitin da ake cewa an kafa ne ya yi bincike, bayan ya tattauna da dukkan bangarorin da abin ya shafa, ya zama ya fitar da rahotonsa, sai ya gano cewa haka aka yi. Sai ya dauki bangare. Ba a yi wannan ba. Amma duk da haka fa ya ce ba zai ce komai ba sai bayan kwamitin ya mika rahotonsa. Kun ga tun yanzu kafin kwamitin ya fara zama, har an ji sakamakon aikinsa ko?

ALMIZAN: To, me za ka ce kan Kwamitin da Majalisun Dokoki da Hukumar kare hakkin bil’adama suka kafa?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa, muna sa ido mu ga me za su yi tunda karkashin gwamnati take. Domin abin da jiya ta yi, shi za mu fassara yau da shi. Lokacin da aka kashe ’ya’yan Malam ta shigo cikin maganar, ta ce za ta bincika, amma har yau ba wani abu da ta yi. Amma kamar Majalisu tunda su zaman kansu suke yi, insha Allah muna sa ran za su yi wani yunkuri. Ko ba komai maganar ta je Majalisa kuma ta yi wa wasu zafi da ciwo, kuma sun tausaya. Kuma sun gayyace mu mun je mun ba da bahasi. Muna sa ran insha Allah da taimakon Allah za su yi abin da ya dace. Su muna da kyakkyawan fata a kansu.

ALMIZAN: Akramakallah, ya za ka kwatanta irin wannan ta’addancin da sojoji suka yi?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Wannan ta’addancin da sojoji suka yi ni ban san yadda zan kwatanta shi ba. In ka ce masa dabbanci, dabbobi na iya kai ka kara. Domin su ba su kashe junansu haka. In ka ce masa hauka, mahaukata na iya kai ka kara. Don mahaukata ba sa yin haka nan. In ka ce zalunci, sai a ce maka abin da aka yi a Zariya ya fi karfin zalunci. Domin zalunci masu rai ake yi wa, amma wannan har da matattu da ke cikin kaburbura aka yi wa. Ban san me zan ce masa ba. Su kawai suka san me suka yi. Ban san ko suna da kalmar da za su kira abin da suka yi ba.

Alal misali mu kaddara Shi’a muke yi, wacce ka’ida ce, ko doka ce ta ce shi dan Shi’a kashe shi ake yi? Kuma in za a kashe shi, ba a kai shi kotu a ji ya yi laifi, ko bai yi ba, sai kawai a sa bindiga a harbe shi? Yaushe aka yi dokar cewa Shi’a ta zama laifi a kasar nan? Yaushe ne gwamnatin kasar nan ta zama ta Sunna, kuma za ta yaki Shi’a? Tambayoyi ne da ya kamata su karba. Wadannan kashe-kashen da suka yi ba a san da me za a kwatanta su ba.

Wannan abin da suka yi ya yi kama da ta’addanci. Amma shi ta’addanci wadansu mutane ne sukan kai hari wani wuri saboda su biya bukatarsu ta siyasa. Kamar su kai wani hari a wata masana’anta, ko wani ofishin gwamnati, ko ofishin siyasa, ko kasuwa don cimma muradinsu na a daina yi masu kaza, ko kuma a yi masu kaza. Wannan ba ko daya. Me kuke so a yi? Babu. Me kuke so a bari? Ba su fada ba. To, ka ga ko da an ce masa ta’addanci ma, to su ’yan ta’adda ga yadda suke nasu. Har yau ba su fadi dalili ba. Dalilan da suka bayar suna karo da juna.
Gaskiya an yi mana abin da ya fi karfin zalunci. Kisan mata da yara da tsofaffi. Kuma ga wadanda ba su da ko allura. Kaddara ma wani ya dauko sanda, ko gwafa, a mandiki irin na wannan zamanin tsakanin mai bindiga da kuma wanda ya rike wadannan abubuwan, wa ke dauke da makami? Idan ka ce ai shi ma makami ne, sai mu ce to cikin biyun nan, wa ya kashe wani? Sannan kuma me ya kai a jefa gurneti a gida? Shi fa ana jefa shi ne a fagen daga tsakanin sojoji masu karfin makamai iri daya da tirenin iri daya. Saboda haka sai a wurga gurneti don a kara gaba a je a kama sansaninsu. Wannan a gidan kwanan mutane ake ta wurga gurneti, kuma mutane na ciki. A wajen taron jama’a suka wurga, kuma akwai mata da yara a wajen.

Kuma sojojin sun yi kisa da rana, wanda ake kira ‘massacre’, sannan suka yi kisa da dare da suke kira ‘genocide’, suka yi ‘state killing’ kuma, wato a ayyana wasu mutane, wannan da wancan su ake so a kawar. Kamar ’ya’yan Malam guda shida din nan da aka kashe, ‘state killing’ ne. Da wane dalili? Me ya yi zafi haka? Duk da cewa mutanen nan suna da amfani a kasa, ’yan kasa ne masu ilimi, kuma ana sa ran za su amfanar da al’umma a nan gaba. Ka ga har kasar ma an yi mata hasara. Don cikin mutunen nan da aka kashe din nan, akwai Likitoci, Injiniyoyi da kuma wadanda suke kan hanyar kammala karatunsu. Wannan zagon kasa ne ga kasa. Ya kamata a kama su a hukunta su da laifin cin amanar kasa.

Idan ma ana ganin kamar Shi’a barazana ce, ai akwai wasu kungiyoyi a duniya da ake ganin su a matsayin barazana, kamar IRA a Birtaniya, sun shekara sama da 100 suna fada da gwamnatin Landon da makamai. Amma yanzu sun zauna suna tattaunawa. Masu mamakai suka ajiye, aka yi yarjejeniyar zaman lafiya.

A Colombia akwai kungiyar da ta kwashe fiye da shekaru 50 tana yaki da gwamnati, a lokacin da ake cikin daji ana fada, akwai kuma wasu suna hawa kan teburin shawarwari suna tattaunawa. Har ma an cimma matsaya, yakin ya kusa zuwa karshe.

A Phillipines akwai wasu Musulmi da suke jagorantar wata kungiya da suke neman ballewa daga kasar saboda ana takura su. Su ma kusan sama da shekara 20 ana fafatawa. Amma da aka hau kan teburin shawarwari, an cimma matsaya, har yakin ya tsaya ba ka ji ana bude wuta.

Haka kuma akwai wadanda suke da’awar za su balle daga kasar nan su kafa kasar Biafra. Sun yi kudi, tuta da fasfot dinsu, suna tare motoci, suna kashe mutane, suna yakar sojoji, suna kashe ’yan sanda. Shugabansu ma da aka kama yana gudanar da gidan rediyo da yake yada manufofinsu, kwanan baya an ba da shi beli, sai dai ba a sake shi ba ne kawai, saboda abin da Buhari ya bayyana barazana ga zaman lafiyar kasa. Ka ga an san shugabanninsu, kuma ana iya tattaunaw da su, ana kuma lallashin su.

Sannan kuma ga Neja-Delta, mutanen wannan yankin an san su da kiyayya da kasantuwar kasar nan a dunkule, sun yi ta yunkurin ballewa. Suna ganin arzikin kasar nan gaba daya nasu ne. A kwama da su. Sun yi ta kai hare-hare, sun kashe sojojin da ba a san adadinsu ba. Amma yanzu albashi ake ba su ana lallashin su. Har da Ma’aikata sukutum da guda aka kafa mai kula da su.

Ga kuma wannan kungiyar da ake kira Boko Haram, tare da cewa an kwashe shekaru shida ana yaki da su. An kashe dubban mutane, ciki har da sojoji, miliyoyi sun bar gidajensu, an lalata garuruwa masu tarin yawa. Amma mun ji ko a wannan Media Chat din Buhari yana cewa idan har ya samu shugabanninsu zai tattauna da su.  

Haka ake yi a duniya. Idan akwai wata kungiyar da ake ganin barazana ce ga zaman lafiyar kasa, sai a nemi jagororinta a zauna da su. A ji meye bukatunku? Me kuke so? Mu kuma ba barazana ba ce ga kowa. Shi Buharin bai san Harka tana da jagoranci ba ne? Idan wani abu ya faru me ya sa ba zai neme su ba? Tunda shi da kansa ya ce an ba shi labari sama da shekara 20 ana takura wa mutane. Ka ga muna nan sama da shekara 20 ke nan? Me ya sa bai nemo mu a tattauna ba, sai kawai aka auka mana, aka yi mana kisan kare dangi? Ka ga wannan ya nuna maka shiryayyen abu ne, mune ba a so, mune ake so a kawar. Illa iyaka. Ba wani uzuri da za a ba mu.  

ALMIZAN: Yanzu gaba daya Akramakallah me muke bukata?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Abin da muke bukata shi ne; Na farko a saki Malam da iyalansa da sauran wadanda ake tsare da su ba tare da sharadi ba. Na biyu a ba mu marasa lafiyarmu mu yi masu magani. Na uku a ba mu gawawwakinmu, mu yi masu jana’iza daidai da yadda addinin Musulunci ya tanada. Na hudu a kafa kakkarfar Hukumar bincike mai zaman kanta, wadda za ta kunshi mutane masu mutunci. A yi bincike, tun farko ma me ya sa ake kai mana hari? Mene matsayarmu, mene ne matsayar gwamnati? Daga nan kuma abin da zai biyo baya sai ya zo, irin su biyan diyya na rayuka na dukiya, ba da hakuri, mai da mana muhallanmu da sauransu.

ALMIZAN: Akwai wani sako da kake shi ga ’yan uwa?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: ’Yan uwa ,kamar yadda muka sani muna da tsari wanda Malam ya dora Harkar nan a kai. Ina kira gare su a lizimci wannan nizamin. Da fatan duk abin da ake gudanarwa kar komai ya tsaya. A ci gaba da komai bisa nizami da tuntuba. A dage da addu’o’i sawa’un a dai-daiku ne ko haduwa waje daya a yi. Sannan a guji jita-jita. Kar mu mai da Social Media wajen amsar umurni. Ba a nan ake samun umurnin yin kaza, ko barin kaza ba. Kar ya zama wance kaza Media ta ce a yi kaza. Akwai sakonnin da akan bayar ta wadannan hanyoyin, amma da cikakken suna na wanda ya bayar din. Idan aka yi ‘program’, ko wani jawabi ana iya yada shi ta wannan hanya din, yana da kyau. Amma magana da yawun Harka, ya kamata a san daga ina za a yi. A lokacin taron da aka yi a kan Tattaki su Malam suna cewa ba kowa ne ke ba da sanarwa ba. Ya ce, duk wanda zai bayar da wata sanarwa wajibi ne ya zama an san waye shi, domin ba kara-zube muke ba.

Yana da kyau ’yan uwa su san cewa duk wadannan abubuwan da ake yi mana ana kokarin tunzura mu ne domin mu yi wani abu da ya saba wa hadafin Harka. Kar ’yan uwa su yarda a yi amfani da su wajen biyan bukatar makiya. Mun saba da waki’o’i. Yanzu mun taka wata marhalar ne. Wannan marhalar ba irin ta baya ba ce. Da DPO ke rigima da mu. Da abin ya fi karfinsa, ya mai da mu wajen Area Commander. Daga nan aka koma wajen Kwamishina. Abin ya koma wajen su AIG. Aka koma hannun IG. Yanzu fa ana maganar Janarori ne, ba kuma Janarorin ba kawai, ana maganar kasa da kasa ne. Akwai hannun manyan kasashe nwaje a ciki. Wannan abin da aka yi mana kowa ya san ‘interest’ din Amurka da Isra’ila ne. Yanzu duniya ce ke yakar mu. Don haka a irin wannan murhalar ana bukatar hankali da natsuwa da kuma hangen nesa kafin a dauki matsaya. In ba haka ba za mu yi abin da zai biya masu bukata cikin sauki. Dole ne ya zama abubuwanmu bisa tsari ne.

A baya idan irin wannan ta faru, muka yi Muzaharori, muka raba ‘release’, sai ka ga abubuwan sun kwaranye. Amma yanzu ka ga yadda ake ta yin Muzaharorin a sassa daban-daban na duniya, amma makiya sai kara azazzala abin suke yi. Don haka yana da kyau ’yan uwa su fahimci cewa yanayin ya sauya, siyasar ta canza. Yanzu ana maganar yakin kwakwale ne. Don haka duk abin da muke yi na Muzaharori da sauransu ba za mu fasa ba, har sai an sako mana Jagoranmu. Kuma za a ci gaba da bin wasu hanyoyin na daban. Abin da Malam ya dora mu a kansa za mu ci gaba insha Allah.

Wani abu muhimmi da nake so in tunatar da ’yan uwa shi ne, tunda mutanen nan sun kara matsawa kusa da Shedan, mu kuma sai mu kara matsawa kusa da Allah. Mu yawaita Azumi da Sallolin dare, in da muna da kasala yanzu mu kara kaimi. In da muna da ragwanci, yanzu mu zabura. Mu yawaita addu’a da sadaka. Wadannan suna sassauta bala’i. Mu yi ta karanta Hasbunallah Wa Ni’imal Wakil 1,000. Salatin Annabi 1,000. Lahaula 1,000. In mutum zai iya yi a zama daya falillahil hamdu, in kuma ba zai iya ba ya dauki daya ya yi dubu yau, gobe da jibi ma haka. Sannan kuma akwai Ya Kaharru 306 bayan Sallar Asubahi kafin mutum ya tashi daga wajen, da nufin Allah ya ba mu rinjaye a kansu, ya kuma kwato mana Malam da dukkan wadanda suke tsare. A rika ziyartar bayin Allah suna yi mana addu’a, Allah yana amsar addu’arsu.

In da so samu ne, duk wani dan uwa mai hali a cikin mu, ya zama tsawon mako guda daga Juma’a zuwa Juma’a ya samu gidan mutane uku gajiyayyu ya jibanci abincinsu na wuni guda. Wannan ya yi, wannan ma ya yi. Mu kuma sauran ya-ku-bayi wane irin taimako za mu yi wa al’umma a cikin babu dinmu? Allah zai kalle mu da karin rahamarsa, kuma zai kawo mana saukin wannan bala’in. Mu yawaita istigifari, mu kimtsa kanmu, mu dawo cikin hayyacinmu. Duk abin da muka yi da, Allah bai so mu daina, wanda muka san yana so mu kara. Ba mu da wani karfi sai wajen Allah, kuma da sannu zai kawo mana mafita.

ALMIZAN: Ga suran jama’a fa?

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Kiran da za mu yi masu shi ne, su yi mana abubuwa guda biyu. Na farko su taimake mu da addu’a. Saboda wannan abin ba mu kadai ake nufi ba, in an gama da mu kansu aka yo. Mun ga yadda aka ce ana fada da Mai Tatsine a shekarun baya. Daga baya mun gano cewa an yi haka ne da nufin a rage yawan Mahaddata Alkur’ani. Saboda ita kasar tana da shaukin addini. Sannan yanzu suka kafa wata kungiya da suka tsattsamo mutanenta daga kungoyoyi daban-daban suka kira ta Boko Haram, suka kawar da su, yanzu su suke yin aikin da kansu. Yanzu kuma sun zo kan wadanda suka kira ’yan Shi’a, kuma suna so su kawar da su. Bayan nan kuma tunda dai kasar nan ta addini ce, za su hari wasu kuma. Madamar akwai addinin Musulunci, ba za su daina dira a kan Musulmi ba. Kar mutane su ji cewa daga gare mu an gama.

Abu na biyu kuma mutane su rika yi mana adalci. Su kalli ayyukanmu da maganganunmu su rika yi mana hukunci da su, su kuma saurari abin da makiyanmu masu fada da mu suke fada, sai su kwatanta da maganganu da ayyukanmu. Idan mutum ya dauki shaci-fadin gwamnatin ko makiyanmu ya aibata mu da shi, zai tsaya gaban Allah, kuma zai karba tambaya.

ALMIZAN: Akramakallahu mun gode. 

SHAIKH YAKUBU YAHYA: Ni ma na gode kwarai da gaske.288

Almizan