Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkarmusulunci a Nigeria
Asabar

16 Janairu 2016

16:09:11
730769

Ina gani sojoji suka tafi da Shaikh Zakzaky - Cewar Danladi Yakubu da aka sa wa wuta

Jaridar Almizan ta harshen Hausa ta rika gabatar da hirarraki da bangarori daban daban na al'umma bayan hare-haren da sojoji suka kaiwa Harkar Musulunci da kutsen da aka yiwa jagoran Harkar a gidan sa dake unguwar Gyallesu Zariya. Ga wata hira da Almizan tayi da wani wanda yaga lokacin da aka tafi Malam.

ALMIZAN: Za mu so ka bayyana wa masu karatu sunanka.

DANLADI YAKUBU: Sunana Danladi Yakubu Gyallesu.

ALMIZAN: Danladi mun gan ka da rauni a hannunka, me ya faru da kai ne?

DANLADI YAKUBU: Sad da Sojoji suka iso gidan Malam Zakzaky (H) suna ta cewa, ‘a fito! A fito!’ Sai ba a fito ba. Suna ta harbi. Sai suka sa ma gidan wuta. Lokacin sai wuta ta kama ni. Sai suka shigo gidan. Duk wanda wuta ta kama shi, sai su kashe wutar su daure shi. Haka suka yi ta yi wa mutane. Suka daure mu, suka aje mu a gefe, mu ashirin da shida ne.

ALMIZAN: Bayan sun aje ku a gefe, me ya faru?

DANLADI YAKUBU: Malama Zinatu na tsaye, sai wani soja ya kai mata mari, sai ta duke, ita kuma ta kai masa mari, ta same shi. Ya ja da baya, ya noshe ta a ido, sai da wurin take ya kumbura. Ita kuma Suhaila suna so su kama ta, sai abin gagara, sai da suka yi mata taron dangi, sannan suka kama ta suka daure ta. Suna son su harbe ta, sai Malama Zinatu ta ce don Allah kar su harbe ta, su bar ta, ni ku kashe ni. Kun kashe mani yara uku a kwanan baya, kuma yanzu kun karasa sauran don Allah ku harbe ni. Shi ne sai suka harbe ta a gefen ciki.

ALMIZAN: A lokacin Malam Zakzaky (H) yana ina?

DANLADI YAKUBU: A lokacin Malam yana ta sallah da addu’o’i sad da suka shigo gidan. Kuma ana kiran sa ta waya yana amsawa. Kuma ya ci gaba da sallah, da ya kammala, sai suka ce ya tashi su tafi. Sai ya ce harsashi ya goge ni a kafa, ba zai iya tashi ba, sai suka dauke shi suka sa shi a mota, suna ta gaggaya  masa bakaken maganganu, suka fita da shi ta baya. Ita ma Malama suka tafi da su.

ALMIZAN: A lokacin ya ka ga su Malam (H) suke?

DANLADI YAKUBU: Malam ya birge ni. Shi Malam sam babu wata fargaba a tare da shi. Kuma yana waya da wasu suna cewa ya kamata ya bar gidan, ya ce shi babu inda za shi. Cikin izza suka tafi da Malam.

ALMIZAN: Ina su Sayyid Ali da ’yan uwansa?

DANLADI YAKUBU: Sayyid Ali ya yi shahada da Hammad a gabanmu. Sai Sayyid Humaid shi kuma ya fito a guje ya bi sojojin, daga nan ban san inda suka yi da shi ba.

ALMIZAN: Bayan nan kuma ya aka yi da ku?

DANLADI YAKUBU: Bayan sun fito da mu, sai suka dinga dukan mu. Sai ga wani soja ya zo yake cewa tunda an kama mu a gidan Malam, an kama mu waje mai hadari, don haka kashe mu za su yi. Sai suka ba kowa harsashi a hannunsa, wanda da shi ne za su kashe shi. Suna ta dukan mu, suka bar mu a nan. Da suka dawo, sai suka amshi harsasan, suka ce mu kwakkwanta. Suka kwance daurin kafa, sai suka yi ta harbi sama. Mun yi tsammanin ’yan uwanmu suke harbi, kafin a zo kanmu.

Daga nan sai su ka kwashe mu suka kai mu Bariki cikin defot, suka saka mu dakin kasa (underground) suna ta dukan mu, sai wani soja ya zo baba, ya ce su daina bugun mu, a dau sunayenmu da shekaru. Bayan nan sai suka fito da mu wani fili, suka shanya mu fili. Akwai sanyi sosai, suka daure mu, suka kwantar da mu kasa. Sai suka dauke mu suka kai mu wani daki. Cikin dakin akwai sitoci da yawa a ciki, da yara kanana. Sai Sista Zainab da suka kama a gidan Malam, ba su sa ta ciki ba. Daga can baya suka aje ta, suka sa wani abu kamar keji, suka hana kowa zuwa wajenta, sai su ke zuwa suna mata tambayoyi.

Ranar Talata sai suka zu su dauke mu suka ce za su kai mu asibiti ne. Sai suka kai mu asibitin Shika, kuma suka ce kada wanda ya ba mu waya; idan wani ya ba mu waya za su buge shi. Daga nan, sai wani babban soja ya zo ya ce, duk wanda aka yi ma aiki a ba shi waya, ya kira ’yan uwansa, su zo su tafi da shi. Sai ga Malaman unguwarmu suka zo suka tafi da ni.

ALMIZAN: Wane abu ne ya fi ba ka tausayi a cikin wannan ta’addancin?

DANLADI YAKUBU: Abin da ya fi ba ni tausayi shi ne, yadda sojojin suka yi ta harbi ba kakkautawa. Kuma a nan gidan Malam, sai wani yaro wanda bai wuce shekara daya ba, ina jin an kashe mahaifiyarsa ne ya hango wani soja, ya taho wajensa, yana ga Baba, ga Baba, sai kawai sojan nan ya dauke yaron nan da bindiga. Wannan abu ya girgiza ni matuka.

ALMIZAN: Meye kiranka ga ’yan uwa?

DANLADI YAKUBU: Su dage da jajircewa. Wannan Harkar haka take. Idan mutum na tsoron mutuwa kar ya shigo. Kuma ya kamata ’yan uwa su dage da yi wa su Malam addu’ar Allah ya ba su lafiya, kuma ya fiddo su lafiya, mu kuma ya ba mu juriya da tabbatuwa a kan wannan Harka, amin. 288

Jaridar Almizan