Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Asabar

16 Janairu 2016

11:11:23
730724

Yunkurin sojoji na boye gaskiyar abin da suka yi - Ishara akan nasarar jini akan makami

Babban abin da sojojin Nigeria suka sa a gaba a yanzun kuma suke sarrafa kudi mai yawa a kai shine shirya karerayi da Farfaganda ta karya don su boye mummunan kisan kiyashi na rashin tausayi da suka tafka akan Harkar Musulunci a Nigeria da kutsen da suka yi zuwa gidan jagoran Harkar Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

A gidan sa dake unguwar Gyallesu, tare da irin dukkanin keta, da take hakkin bil adama da suka nuna bayan kisa da keta ka'idoji na musulunci da na mutumtaka.

Yanzun kuma sai bin hanyoyi ko wane iri suke yi don ganin sun rufe wannan mummunan ta'addanci da kisan kiyashi da tarihi ya riga ya rubuta.

Sojojin suna amfani da kafafen yada labarai, da suka hada da radiyo, talbijin, jaridu, da dukkanin karfin su wajen cusa karereyi da murguda hakika don su cimma wannan burin.

Haka nan kuma suna amfani da hanyar sayen wasu daga cikin malaman kasar da shuwagabannin al'umma domin su yi amfani da su wajen tallata abin da suke so, na rufe barnar da suka tafka da kuma canza abin da suka yi, kisa da keta alfarma da rana tsaka kowa na gani.

A ranar Alhamis din nan 14 ga watan Janairu 2016 shugaban sojoji na 1 Mechanized Division Major General Adeniyi Oyebade ya kira wani taro wanda aka gayyaci wasu daga cikin shuwagabannin kungiyoyin musulmi, da wasu daga cikin Hakimai da Dagatai, inda yayi iya bakin kokarin sa na gamsar da su, su fahimci sojoji game da harin da suka kai a Zariya.

Bayan an kammala taron kuma an bi dukkanin mahalarta da kudi Naira #500,000.

Ya kamata ne jarumi in yayi jarumta ya fito fili ya ce yayi, ba tare da tsoro ko razani ba. Amma irin wannan matakai da sojoji suke dauka ya kara nuna irin kasantuwar su ragwan maza.

Sun dauki sama da awa talatin suna harbi da kisa akan mata, yara da mutane da babu komai a hannun su sai duwatsu na kare kai, kuma yanuzn sun kasa fitowa su ce sun yi. Sai kame-kame suke yi suna rawar jiki suna kokarin boye abin da suka yi ta ko wacce hanya.

Tun a nan ma mun kara ganin cewa tarihi yana maimaita kansa na cewa "Jini yayi nasara akan makami" kamar yadda ya faru shekaru sama da dubu da dari uku a Karbala.288