Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Alhamis

14 Janairu 2016

17:24:34
730522

Dalibai 'yan makaranta sun ci gaba da kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa

Bangaren dandamalin dalibai na Harkar Musulunci ko "Acadamic Forum" sun ci gaba da gabatar da gangami na dalibai 'yan makaranta zalla a cikin ci gaba da ake da kiran #a saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa ba tare da wani sharadi ba. Mahalarta wannan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky.

Suna Kabbara suna rera taken a gaggauta sako mana jagora maulan mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Dukkanin wadan nan gangami ci gaba ne da jerin muzaharori da ake gabatarwa a dukkanin fadin kasar da kasashen waje na yin tir da Allah waddai kan hare-haren ta'addanci na sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma kutsen da suka yi zuwa gidan Sheikh El-Zakzaky wanda ya sabbaba shahadar dimbin mutane da kuma jikkita da dama.

Kamar yadda aka sani ne bayan hare-haren ta'addancin na sojoji sun kuma rika bin gine ginen Harkar da suka hada da makabarta, Husainiya da masallaci suna rugurguzawa.288