Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Alhamis

14 Janairu 2016

07:56:24
730426

A karon farko bayan sama da wata guda an sami damar ganawa da Malam

A karon farko bayan sama da wata guda, wata tawaga ta sami damar ganawa da Malam a inda yake tsare, tun bayan hare-haren da sojoji suka kai gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky a unguwar Gyallesu wanda yayi sanadin kashe 'yan uwa masu dimbin yawa tare da jiwa da dama raunuka

Har ya zuwa yau din nan kimanin kwanaki 40 tun daga soma wannan hare-haren ba'a san inda da yawa daga cikin 'yan uwa suke ba. Kamar yadda kuma har ya zuwa yau din nan ba'a baiwa iyalai da dangi gawawwakin wadanda aka kashe ba, don yi musu sutura kamar yadda shari'ah ta tanaza.

Farfesa Dahiru Yahaya na cikin tawagar data sami ganawa da Malam a jiya Laraba 13 ga watan Janairu, 2016 karkashin lemar kungiyar NSCIA kuma bayan ganawar ya bayyanawa 'yan uwa halin da ya ga Malam. 

A wata hira da yayi da tashar talbijin ta Al-Wilayah Farfesa ya tabbatar da wannan ziyarar sannan ya ce zasu ci gaba da kokarin ganin an ci gaba da yin irin ta.

'Yan uwa dai na ci gaba da kira a gaggauta sakin Malam ba tare da wani sharadi ba. Haka nan dukkanin sauran 'yan uwa dake tsare a gidajen kaso daban daban, tare da bada gawawwakin wadanda aka kashe don ayi musu sutura.288