Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Litinin

11 Janairu 2016

20:18:05
730103

An yi muzaharar kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky a yau Litinin a Kaduna

Dazun nan ne a yau Litinin 11 ga watan Janairu 2016 'yan uwa al'ummar musulmi suka gabatar da wata muzahara a garin Kaduna, suna kiran a saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa. Mahalarta wannan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna Kabbara suna rera taken a gaggauta

Sako mana jagora maulan mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Dukkanin wadan nan gangami ci gaba ne da jerin muzaharori da ake gabatarwa a dukkanin fadin kasar da kasashen waje na yin tir da Allah waddai kan hare-haren ta'addanci na sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma kutsen da suka yi zuwa gidan Sheikh El-Zakzaky wanda ya sabbaba shahadar dimbin mutane da kuma jikkita da dama.

Kamar yadda aka sani ne bayan hare-haren ta'addancin na sojoji sun kuma rika bin gine ginen Harkar da suka hada da makabarta, Husainiya da masallaci suna rugurguzawa.288