Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Talata

5 Janairu 2016

16:55:40
728930

Kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky - 'Yan uwa mata sun gana da manema labarai a Kaduna

'Yan uwa mata al'ummar musulmi daga garuruwa daban daban na Nigeria a yau Talata 5 ga watan Janairu sun fito sun gabatar da muzahara ta lumana suna kiran a saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa. Mahalarta wannan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna Kabbara suna rera taken a gaggauta.

Sako mana jagora maulan mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Dukkanin wadan nan gangami ci gaba ne da jerin muzaharori da ake gabatarwa a dukkanin fadin kasar da kasashen waje na yin tir da Allah waddai kan hare-haren ta'addanci na sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma kutsen da suka yi zuwa gidan Sheikh El-Zakzaky wanda ya sabbaba shahadar dimbin mutane da kuma jikkita da dama.

Kamar yadda aka sani ne bayan hare-haren ta'addancin na sojoji sun kuma rika bin gine ginen Harkar da suka hada da makabarta, Husainiya da masallaci suna rugurguzawa. 

A Kaduna bayan kammala gangamin 'yan uwa matan sun gana da manema labarai.288