Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : harkarmusulunci a nigeria
Litinin

4 Janairu 2016

14:28:45
728707

Kiran #A saki Sheikh El-Zakzaky ya shiga marhala ta gaba - An fito a Abuja

Dazun nan ne a yau Litinin 4 ga watan Janairu 2016 dubban 'yan uwa al'ummar musulmi suka gabatar da wani gangami a garin Abuja babban birnin Nigeria, suna kiran a saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa. Mahalarta wannan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna Kabbara suna rera taken a gaggauta

Sako mana jagora maulan mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Dukkanin wadan nan gangami ci gaba ne da jerin muzaharori da ake gabatarwa a dukkanin fadin kasar da kasashen waje na yin tir da Allah waddai kan hare-haren ta'addanci na sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma kutsen da suka yi zuwa gidan Sheikh El-Zakzaky wanda ya sabbaba shahadar dimbin mutane da kuma jikkita da dama.

Kamar yadda aka sani ne bayan hare-haren ta'addancin na sojoji sun kuma rika bin gine ginen Harkar da suka hada da makabarta, Husainiya da masallaci suna rugurguzawa.288