Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : mu'assasatul thaqlain
Jummaʼa

1 Janairu 2016

17:07:30
728021

TSOKACI DA SHAWARWARI GAME DA WAQI’AR ZARIYA,KASHI NA BIYU (2)

NA SHAIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL YUSUF SULAIMAN YA RUBUTA

…..cigaba. Ba wai mun ce muna cikin Islamic Movement bane a yanzu,mun wuce shekara goma sha shida da fita daga cikin Islamic Movement,amma muna kallon abin ne  a matsayin insafi da adalci.Wannan zai iya samun kowa,kowa zai iya samun shi.Kuma ana yin shi,wato ba BID’A bane.Abin da nake nufi ba kagagge bane,kuma ba farau bane.Ana yin irin wadannan abubuwan a wurare daban daban,saboda haka wannan babban kuskure ne. Kuskure na gaba wanda sojoji suka yi,shine yanda suka yanke ma kansu akan cewa yaki zasu yi da ‘yan uwa Musulmi din.Kuma daga hujjoji da kuma abubuwan da shi Col Sani Usman Kukasheka ya dinga fadi.Wannan ba a wannan hoton mai motsi na gani ba,a labarai da jaridu da kafafen yada labarai daban daban-sun riga sun dauka,ya riga ya zama hujja ya kuma zama tahiri ya zama dawwananne abu. Na farko;Col Sani Usman Kukasheka yace wannan yunkuri ne na hari na kisa akan Shugaban rundunar sojojin Nigeriya,abu na farko da ya fadi kenan. Na biyu kuma yace wannan yunkurin da umurnin Shaikh Zakzaky ne. Sannan na uku yace bai kamata a bar wannan abin ya maimata kan shi ba. Sannan na hudu yace wannan abin ba zai tafi ba tare da anyi ukuba akan shi ba. Sannan na biyar yace za su bi RULES OF ENGAGEMENT na soja-wannan yana nufin kenan yaki ake so a yi. To!wadannan kalmomi ko jumloli jeri bayan jeri har guda biyar sun nuna akan cewa kaman sun dauki mataki zasu yi yaki da su ‘yan uwa Musulmi din.Wannan babban kuskure ne muke gani wanda ya kamata a kalle shi sosan gaske.Harshen mu shine harshen ishara,harshen mu shine harshen nasiha,harshen mu shine harshen neman warwara da daukan darasi domin gaba. To!lokacin da suka dauki wannan matakin sai ya zama yakin suka yi.Karfin da aka yi amfani dashi akan ‘yan uwan akwai alama akan cewa na farko kila an gwada su ne akan cewa suna da makamai,saboda wanda yake da makami ne ake daukan mashi irin wannan matakin.An gwada su ne a gani in suna da makamai sai su fito dasu.Sannan kuma na biyu zai iya yiwuwa a lokacin wasu sun so sojoji su yi masu aikin su wato kila an tinzira su(sojoji)ne su yi wa wasu aikin su wato wadanda suke gaba da su ‘yan uwan.Ba mu da hujja akan wannan.Muna karanta waqi’i ne wato REALITY.Zai wahala a dauki irin wannan matakin da wannan karfin wanda ya wuce hankali akan mutanen da suke makaman da aka ce suna dasu sune duwatsu da gofa da adduna da sauransu. Wani kuskure da soja suka yi shine yanda ya zama suka bar ita Husainiyyar bayan sun yi abin da suka yi,suka tafi gidan Shaikh Zakzaky.Sai ya zama cewa awa wajen talatin suna yaki a gidan,suna harbi da sauran su da sauransu,suka rusa gidan gabaki daya,sannan suka wuce Makabartar su.Wanda wannan ke ishara kila wasu ne suka nuna masu wuraren ko kuma suna ma wasu aikin su ne.Wadannan din basu yi kyau ba kuma ya kamata ya zama cewa a bincike su.Kila in dawo zuwa ga wannan a gaba in na zo ina so in ba da shawarwari ko abin da yayi kama da haka. Ta janibin su ‘Yan uwa Musulmi,akwai kurakurai masu yawa wa’yanda su ma suka yi.Babban kuskure ko kuma daya daga cikin manya manyan kuskuren da ‘yan uwa musulmi suka yi shine wannan abin bakin cikin da na fadi na cewa wannan irin gaggarimin taro wanda za a yi amma sai ya zama cewa ba a yi ANTICIPATING wato ba a hango cewa za a iya samun irin wannan yanayin wanda shugaban sojoji zai zo wucewa ba.Sai ya zama wadanda suke a lokacin ba su wuce wanda zaka ce masu AREA BOYS din ba.Ko da an ajiye masu gadi a wajen-wanda yana da kyau a ajiye masu gadi a wajen-to ya kamata ya zama cewa suna da iyaka ya zuwa ga abin da zasu iya zartarwa a nan take a lokacin.Dole ne ya zama akwai abin da ake ce CHAIN OF COMMAND wanda yake ayyananne sananne tabbatacce,kuma kowane level na wannan chain din ko kuma kowane KNOT na wannan chain din,ya kamata ya zama cewa an ayyana mashi iyakar karfin abin da zai iya zartar wa,in ya wuce wannan ya kai gaba,ya kai gaba har zuwa ya kai ga shi Malam din. Bai kamata ya zama wadannan wadanda suke a wannan wurin wadanda aikin su shine gadi da bada labarai ya zama cewa za su iya daukan kowane mataki,saboda akwai abin da ya fi karfin su.Akwai ababe da ya kamata da a ce suna mika wa ne gaba,domin a gaya masu abubuwan da suka fi saboda ayyukansu shine wannan gadi din da bada labarai.To!amma sai ya zama cewa su suka dinga daukan matakai har abin da ya faru ya zama ya faru.Wannan kuskure na farko kenan a ra’ayin mu. Kuskure na biyu,shine yanda aka yi ba su iya karantar lugan soja din ba a lokacin da suke wannan lugan.Suka fadi wadannan abubuwan guda biyar,cewa: Yunkuri ne na daukan rai na COAS. Sannan da umurnin Malam Zakzaky ne yunkurin ya taho. Sannan kuma ba za a bari ya maimaitu ba. Sannan dole sai an yi ukuba akai. Sannan za a amfani da RULES OF ENGAGEMENT. Lokacin da a ce sun iya karanta wannan lugan suka fahimci cewa luga ce ta yaki,da sun iya dauke Malam tun da suna da lokaci daga lokacin da abubuwan suke faruwa a Husainiyyah zuwa lokacin da sojojin suka tafi Gyellesu.Suna da lokacin isashshe da zasu iya dauke Malam din daga wurin sai ya zama cewa-in da an dauke shi din,kila da zai zama sai ya dinga bada umurni,kila ya samu hanyoyin sadarwa ga su sojojin da abubuwan da suka yi kama da wannan.To! amma ‘yan uwan kila ba su taba tsammanin haka ba zai iya faruwa ba,suna ganin sun wuce haka ya same su saboda haka sai suka yi sakaci mai tsadan gaske wanda ya jawo abin da ya faru a yanzu. Sannan ban da haka kuma,lokacin da sojoji suka tafi Gyellesu,da sun bar su masu gadin ne kawai,maimakon su ce kowa da kowa,dukkan ‘yan uwa gaba dayan su dole su zo Gyellesu.Ya kamata ya zama akwai tsare tsare masu yawan gaske.Ba dole ‘yan uwa su same abin da nake fadi yanzu ya zama ya gamsar dasu ko sun ji dadin shi ba ko abin da yayi kama da wannan.Ina da ‘yanci akan ra’ayi kuma haka na hanga kuma abin da ya faru dole ya shafe mu saboda akidar da suke da’awar suna yin ta,muma ita muke akan ta wato kenan shi’anci.Saboda haka ya shafe mu,kuma akwai abubuwan da muke ganin ba haka ya kamata ya zama ba,wato in da mune da ba haka zamu yi ba ,amma kuma yanzu duk an tattara mu gabaki daya an ce wannan an yi ne saboda shi’anci,tare  titi an yi ne saboda shi’anci.Yana da kyau a fahimta shi’anci ba shine tare titi ba saboda kowa yana tare titi kamar yanda muka fadi ba a baya-Ba dole bane abin da nake fadi ya zama yayi masu dadi ba,ko kuma su gamsu dasu ba,amma dai muna ganin wannan babban kuskure ne-Da sun dauke Malam,sun bar ‘yan taqaitattun mutane.In ma ana so a rusa gidan ne,da sai su bari a rusa gidan amma ba kowa a ciki maimakon su dinga tahowa gabaki dayan su din nan wanda wannan kila ya kara wa su sojojin kumaji akan su cigaba da yin mu’amala dasu ma’amalar yaki da su ‘yan uwan.Saboda haka aka samu barnar da aka samu mai yawa. Sannan ban da wannan,su ‘yan uwa din yana da ban mamaki ba su iya karanta yanayin –ko da yake za su iya cewa sun karanta yanayin domin da man ana so a afka masu,wato shi COAS ba ya taho bane daga Jigawa saboda wani taro ya taho DEPOT a Zariya ba domin wani taro,a’a akan tsari ne,daman an san zasu yi wannan taron sai aka aiko sojojin domin su yi masu haka.Ba komai ko da suna da wannan ra’ayin.To!amma abin da za a dauka akan su shine tun da kun san haka ne,me yasa kuka yarda ya faru?me yasa kullum kuke sanya kanku a cikin tarko wanda kuke ganin cewa ana dana maku?In kun dauka haka zai faru,me yasa kuka yarda ya faru?Ga shi yanzu wannan yana so ya zama wani abu akan shi’a gabaki daya.Ana shigo da abubuwa daban daban dangane da akidun shi’ah da suke ba akidun shi’ah din bane,suna dankara ma shi’an,suna cewa haka suke albarkacin wadannan abubuwan da suka faru.Ta na nan ne mu ya shafe mu,da kuma ta ‘yan Adamtaka da janibobi daban daban,kamar cewa mu ‘yan kasa ne,mu makwabta ne naku (wato ‘yan uwa musulmi),makwabta ne na sojojin,makwabta ne na mutane da dabakoki daban daban,kasa ta hada mu saboda duk wadannan abubuwan da suke faruwa sun shafe mu.Muna bakin cikin abin da suka farun da rasa rayuka da aka yi da ababen da suka yi kama da haka din.Saboda haka dole ya zama cewa mun yi magana,sannan kuma mu bada shawarwarin mu. Idan mutum yana ganin cewa kamar wannan abin yana da kyau da ya samu su ‘yan uwa din,ya kamata ya daina tunanin yana da kyau din.Muna mai nasiha ya daina tunanin yana da kyau komin sabani wanda kake dashi dasu ‘yan uwan bai kamata ya zama ka ga irin wannan abin ya samu dan Adam ba sannan sai ya zama cewa ka ji dadi –Dan Adam din musulmi ne ko ba musulmi-a matsayin dan Adam muke magana akai,ai muna bakin ciki mu ga a Amerika misali ana zaluntar bakaken fata ba don mu bakake ba kuma duk duniya suna bakin ciki.Wato zalunci a ko’ina ya faru,kowane ne mutumin, ko ka san shi ko ba ka san shi ba,akidar ku daya ko ba akidar ku daya ba.Kai ya kamata ka zama mai taimako ga wanda aka zalunta,ka kuma taimaki azzulumin ta hanyar hana shi zalunci.Bai kamata ka zama SELECTIVE ba a cikin adawa da zalunci da kake yi saboda mutane,ka yi adalci-Adalci shi ya fi kusa da tsoron Allah-Ka lura akan cewa idan aka bari wannan ya faru ya tafi ya wuce tun da ‘yan shi’a aka yi ma wa,to!wannan abin zai sa a halatta yin haka akan kowa sai zama wata rana NAUBAN ta zama NAUBAN ka ta same ka. Saboda haka mutane su kalli wannan a matsayin cewa bai kamata ya tafi hakanan ba.A san yanda za a yi a warware wannan matsalar tun a yanzu,da ma’anar cewa yanzu ya zama a dauki hanya ta warkarwa wato HEALING PROCESS.Duk abin da za a yi ya zama cewa an yi healing din ta dukkan janibobi haka ya kamata a yi.Kaman ta janibin su ‘yan uwa din yanzu ya kamata a ce yanzu su zama cikin IZZA.Da dalilin cewa duniya gabaki daya wato masu hankali a cikin duniya gabaki daya suna magana a madadin su,ko ba suyi magana ba.Yanzu ana magana a madadin su akan cewa abin da aka yi din bai dace ba,saboda haka dole a masu adalci,dole a daukan masu fansa,dole a yi kaza kaza da sauransu.To!ka da su bata wannan GOOD WILL din,ka da su bari wannan goyon bayan da ake masu a cikin duniya gabaki dayan ta ya zama cewa sun shekar da shi. Akwai goyon baya saboda abin yana da sosa rai sosai.To!su tafi da wannan goyon bayan da mutane suke musu,saboda haka su kwantar da hankulansu.Kuma in da Malam na nan kaman haka zai ce,wato a kwantar da hankali-a lokacin da aka kashe mashi ‘ya’yan shi abin da yace kenan.Aka ce yanzu me zaka ce?yace ‘yan uwa su kwantar da hankalin su.Kuma a wannan ma da ya farun,an  yi  fira da shi a radiyo ya fadi cewa a kwantar da hankali-ba nace ka da nemi hakkoki bane amma dai a san yanda za a yi,ka da ‘yan uwa musulmi su bar area boys su zama cewa sun dauki harka a hannun su.Dole ne ya zama cewa akwai shuwagabanni a cikin harkan yanzu ko kuma wasu su mai da kansu su zama shugabanni dole su daukan ma kansu wannan nauyin dole na tafiyar da wannan al’amarin na harka a yanda ya dace.A yi amfani da hankali,a yi amfani da basira,a yi amfani da hikma da kwakwalwa wurin warware abin.288