Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Jummaʼa

1 Janairu 2016

16:05:44
728004

Harkar musulunci zata maka gwamnatin Nigeria gaban kotun duniya [ICC]

Harkar musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky zata maka gwamnatin Nigeria gaban kotun manayn laifuffuka ta duniya [ICC] akan irin mummunan ta'addancin da sojojin gwamnatin suka yi akan Harkar da kuma ci gaba da tsare jagoran Harkar Sheikh Ibraheem El-Zakzaky

Malam Yakubu Yahaya Katsina ne ya bayyana haka yayin da yake yin wata hira da manema labarai a cikin wannan makon.

Malam Yakubu Yahaya ya ci gaba da bayyana cewa tuni har an yi Magana da lauyoyi na kasa da kasa wadanda zasu gabatar da kara a gaban kotun ta ICC.288