Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Alhamis

31 Disamba 2015

11:05:57
727796

'Yan uwa musulmi sun nemi #A saki Sheikh El-Zakzaky, mika gawwawaki, sakin na tsare

Rahotannin da suke shigo mana na nuna cewa wakilan 'yan uwa al'ummar musulmi da suka gana da kwamitin majalisar wakilai ta kasa sun nemi a saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, kafa kotu ta musamman don bincike da hukunta dukkanin mai hannu a cikin lamarin

Hare-haren sojoji a Zariya, mika gawawwaki don ayi musu sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada, sakin dukkanin wadanda aka kama aka tsare a gidajen kaso, da sauran su.

Wannan kwamitin dai kamar yadda rahoton ya nuna yayi zaman sa ne a jiya Laraba.

Tuni dai jaridu da mujallu sun fara daukan labarin a fadin kasar Nigeria.

Kamar yadda kowa ya sani dai har yanzun jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky yana tsare a hannun hukuma, duk kuwa da irin raunin da ya samu sakamakon kutsen da sojoji suka yi a gidan sa a lokacin hare-haren.288