Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAUSA.IR
Laraba

30 Disamba 2015

17:50:47
727683

An Gurfanar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Da Wasu Mabiyansa A Gaban Kotu A Kaduna A Jiya Talata

Jami’an yansanda a birnin Kaduna a Nigeria sun bada labarin cewa sun gurfanar da Sheikh Ibrahim El-zakzaky

Jami’an yansanda a birnin Kaduna a Nigeria sun bada labarin cewa sun gurfanar da Sheikh Ibrahim El-zakzaky tare da wasu mabiyansa a gaban kotun majestry mai lamba daya kan titin Zaria, inda suka tuhumesu da laifuffuka wadanda suka hada da cin amanar kasa da kuma tada hankalin jama’a.

Kakakin yansanda Olabisi Kolawole a Kaduna ta tabbatar da wannan labarin ga jaridat The nation ta Nigeria a halin yanzu alkali y adage karar, ya kuma ce a ci gaba da tsaresu a gidan yari.

A makon da ya gabata ne babban hafsan hafsoshin sojojin Nigeria Lt.Gen. Tukur Burutai ya ce sojojinsa sun mika Sheikh Ibrahim ta sauran wadanda suka kama a lokacinda mabiya malamin suka tare masa hanya a cikin makonni da suka gabata.

Hakama babban Inspectan yansanda Mr Solomon Arase ya tabbatar da cewa Malamin yana hanunsu.288