Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : harkar musulunci a Nageria
Lahadi

27 Disamba 2015

07:44:56
727100

Hirar "Daily Trust" da wani da sojoji suka kashewa mutum 5 a cikin iyalan sa

Jaridar Daily Trust da ake bugawa da harshen Turanci kuma take da yawan masu karatu a fadin Nigeria ta samu yin hira da Malam Abubakar Zaki mutumin da sojojin Nigeria suka kashewa mutum biyar cikin iyalan sa a lokacin hare-haren rashin tausayi da suka kaiwa Harkar Musulunci a garin Zariya, da kutsen da suka yi a gidan.............

Jagoran Harkar Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Bayanan da Malam Abubakar Zaki yayi masu sosa rai da tausayi sun sa da dama da suka karanta zubar da hawaye, da sake jin zurfin irin rashin tausayin da sojoji suka nuna a lokacin hare-haren nan.

Malam Abubakar Zaki yayi bayanin yadda ya rabu da iyalan nashi da aka kashe, wanda a cikin su akwai daliba a Jami'ar Abuja wadda take shekara ta biyu a karatun ta, da kuma wadda aka dauka kwalejin tarbiyya dake Zuba, bnda kuma shi surukin sa Muhammad Bello Jega wanda malami ne a jami'ar Abuja.

Ga shafin Hirar:

Shiga ka karanta hirar da Turanci