Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : harkar musulunci a Nageria
Lahadi

27 Disamba 2015

07:40:24
727098

A rana ta 16 da harin Zariya - Ci gaba da gangamin #A saki Sheikh El-Zakzaky a Kano

A jiya Asabar ne a ci gaba da gangamin a saki Sheikh El-Zakzaky, dubban 'yan uwa al'ummar musulmi suka gabatar da wata muzahara a Kano suna kiran a saki Sheikh El-Zakzaky da gaggawa. Maharta wannan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna Kabbara suna rera taken a gaggauta................,

Sako mana jagora maulan mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Dukkanin wadan nan gangami ci gaba ne da jerin muzaharori da ake gabatarwa a dukkanin fadin kasar da kasashen waje na yin tir da Allah waddai kan hare-haren ta'addanci na sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci da kuma kutsen da suka yi zuwa gidan Sheikh El-Zakzaky wanda ya sabbaba shahadar dimbin mutane da kuma jikkita da dama.288