Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Jummaʼa

25 Disamba 2015

12:37:44
726818

Hare-haren sojoji a Zariya - Yanzu kuma an fara dira akan hakkin bayyana ra'ayi

Bayan da sojojin gwamnatin Nigeria suka afkawa Harkar Musulunci a Nigeria da karfin da ya wuce kima kamar yadda da yawa daga ra'ayin al'umma a kasar yake nunawa, tare da yin kutse a gidan jagoran Harkar, Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, yanzun kuma sun fara dira akan 'yancin bayyana ra'ayi daga bangaren Harkar

Musamman ma kamar yadda mai Magana da yawun sojojin Nigeria Colonel Sani Kukasheka Usman ya fito a fili a karon farko ya siffanta daya daga cikin 'ya'yan Harkar kuma daya daga cikin malamai a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya watau Dr Abdullahi Danladi a matsayin wanda ke son ya kawo hargitsi da tada hankali, saboda kawai ya bayyana ra'ayin sa da fahimtar sa kan hare-haren da sojoji suka kawo a Zariya.

Kamar yadda kowa ya sani ne tun daga ranar Asabar din 12 ga watan Disamba, bayan aukuwar wannan hare-haren na ta'addancin bangarori daban daban na al'umma suke ta bayyana ra'ayoyin su, kuma abin da shi Dr. Abdullahi Danladi zai fada ba zai zarce abin da hukumomin kare hakkin bil adama, da daidaikun jama'a suka riga suka ambata ba.

Me yasa mai Magana da yawun sojojin zai nuna yatsan sa akan mutum daya tilo? Shin Dr Abdullahi Danladi ba daya daga cikin al'ummar wannan kasar bane? Ko kuwa kowa yana da ra'ayi da hakkin tofa albarkaci baki ne amma ban da shi?

A iyakar sanin mu Dr Abdullahi Danladi wanda ya kwashe shekaru sama da ashirin yana koyarwa a jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, bai taba samun shaida ta tada hankali ko kawo hargitsi ba, don haka nan babu yadda za'a yi bayan wadan nan shekaru da ya kwashe da Karin kwarewa da gogayya da ya samu kan wannan aikin nashi na koyarwa da tarbiyyantar da dalibai, sai kuma ya koma yana kokarin kawo hargitsi.

Lallai muna ganin a wannan karon bayan take hakkoki da sojojin Nigeria suka tafka, na zubar da jini, da rusa gine gine, da sabbaba hasara ta dukiya suna so ne kuma su dira akan hakkin kare kai da fadin albarkacin baki wanda ake yi ta ruwan sanyi da fayyace gaskiya.288