Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Litinin

21 Disamba 2015

15:24:16
726183

Jana'izar shahidai 6 da 'yan sanda suka kashe a Kaduna

Kamar yadda aka sani ne a ranar Talatan nan data gabata ne 15 ga watan Disamba 2015 jami'an tsaron gwamnatin jihar Kaduna suka budewa muzaharar lumana ta al'ummar musulmim'yan uwa wadanda suka fito gangamin kiran a saki Sheikh El-Zakzaky inda nan take suka kashe wani adadi sannan suka kama wasu

Da ransu suka tafi da su, suka yi ta azabtar da su har ya zuwa shahadar su.

Rahotanni sun tabbatar da cewa cikin irin azabtarwan da aka yiwa wadan nan 'yan uwa da aka kama akwai duka, yanaka jikin su da wuka, shocking, sannan daga bisani suka harbe su.288