Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Litinin

21 Disamba 2015

15:15:10
726178

Sojojin Nigeria sun je sun karasa rugurguza Husainiyar Baqiyyatullah a Zariya

Dama kamar yadda kowa ya sani ne a lokacin hare-haren ta'addancin da sojojin Nigeria suka kaima Harkar Musulunci a Nigeria sun fara da Husainiyar Baqiyyatullah ne, inda kuma suka rusa wani bangre nata suka karkashe wadanda ta rutsa da su a ciki, wadanda dama suka hallara don fara wani buki na daga Tuta.

To yanzun a jiya Lahadi 20 ga watan Disamba 2015 shaidun gani da ido sun ga sojojin sun tafi da irin babbar motar nan mai rusa gini inda kuma suka karasa rusa sauran bangaren da ya rage na Husainiyar ta Baqiyyatullah. 

Dama kuma masu karatun mu sun riga sun san cewa tuni sun gama rugurguza gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky.

Ga hoton Husainiyar Baqiyyatullah nan kafin a karasa rugurguza ta.288