Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA
Jummaʼa

18 Disamba 2015

19:34:38
725662

Muzaharar a saki Sheikh El-Zakzaky a Nigeria, daukain garuruwa da birane sun fito

Rahotannin da suke zuwa mana na tabbatar da cewa a yau Jumu'a 18 ga watan Disamba 2015 daukain manyan biranen Nigeria sun gabatar da gangami ko muzaharar na dubun dubatan al'ummar musulmi mai manufar a saki jagoran mu Sheikh El-Zakzaky. An gabatar da wannan muzaharar a Katsina, Kano, Bauchi, Sakkwato, Jos,

Jalingo, Suleja, Gombe, da sauran birane.

A duukanin inda aka gabatar da wadan nan muzaharori an yi an kammala lafiya. Mahalartan muzaharar sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky inda suke Neman a sake shi.

Haka nan kuma a mafi yawan garuruwan da aka yi muzahararin an rubuta manufar yin muzaharar wanda aka rika rabawa jama'a da manema labarai.

Haka nan kuma manema labarai sun sami damar yin hira da wasu daga cikin mahalarta muzaharar kan manufar su ta yin ta.

Wadan nan muzaharori da gangami zasu ci gaba dai a ko ina cikin kasar har sai 'yan uwan sun kai ga hakkin su na sakin jagoran su Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky wanda har yanzun yake hannun hukuma alhali kuma yana da raunin harbi da bindiga a wurare hudu a jikin sa.

Dukkanin muzaharori suna tafiya cikin tsari da lumana, in banda na garin Kaduna a ranar Talata da ta gabata wanda 'yan sanda suka yi barin wuta akan masu muzaharar wanda ta kai ga kasha wani adadi a cikin su.288