Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HAUSA.IR
Jummaʼa

18 Disamba 2015

19:23:41
725660

Limamin Juma'ar Tehran Yayi Allah Wadai Da Kisan Gillan Da Sojojin Nijeriya Suka Yi A Zariya

Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yayi kakkausar suka ga kisan gillan da sojojin Nijeriya suka yi wa 'yan kungiyar 'yan'uwa Musulunci ta Nijeriya a birnin Zariya yana mai kiran gwamnatin Nijeriya da ta gudanar da bincike da kuma hukunta wadanda suke da hannu ciki cikin gaggawa.

Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a yau din nan inda yayin da yake nuna bakin cikinsa da irin dirar mikiyan da sojojin suka yi wa 'yan kungiyar 'yan'uwa musulmi da kuma kashe wani adadi mai yawa, ya ja kunnen gwamnatin Nijeriyan da guji aikata irin wannan danyen aikin wanda yayi daidai da muradin sahyoniyawa, wahabiyawa da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Boko Haram da Daesh.

Har ila yau Na'ibin limamin Juma'ar na Tehran ya kirayi gwamnatin Nijeriyan da ta gaggauta sakin shugaban kungiyar Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma sauran 'yan kungiyar da ake rike da su.

Bayan sallar juma'ar dai an gudanar da jerin gwanon yin Allah wadai da abin da ya faru a Zariyan, kamar yadda kuma aka gudanar da irin wadannan jerin gwanon a garuruwa daban-daban na kasar Iran.288