A ranar asabar din da ta gabata ne sojojin Najeriya suka yi arangama da ‘yan Shi’a kuma har yanzu an gaza gano hakikanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a tarzomar.
CAN da NSCIA su ne manyan kungiyoyin addini a Najeriya wadanda ke sa ido kan al-amuran da suka shafi Musulmai da Kirista.
CAN ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya shiga cikin lamarin tare da gudanar da bincike game da kisan yayin da NSCIA ta kafa kwamitin mutane bakwai domin gana wa da bangarorin da ke rikici da juna, a wani mataki na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.288