Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : bbc
Laraba

16 Disamba 2015

03:56:21
725154

Amnesty na so a yi bincike a Nigeria

Kungiyar kare hakkin dan-adam ta Amnesty International ta yi kiran a gudanar da bincike mai zurfi don gano adadin mutanen da suka rasa rayukan su, a sa'insar da ta auku tsakanin sojoji da kumayan uwa musulmi a Najeriya

Kungiyar tace kawo yanzu ba ta samu cikakken bayani ba, game da adadin mutanen da aka kashe.

Shugaban kungiyar ta Amnesty International a Nigeria, Ambasada Muhammad Kawu Ibrahim ya ce ya za ma wajibi a hukunta duk bangaren da aka samu da laifi a lamarin domin hana sake aukuwar haka a gaba.

Ya ce dole ne a bai wa wadanda jami'an tsaro suka kama a lamarin damar yin magana da lauyoyinsu, sannan kuma su samu kulawa ta musanman daga jami'an kiwon lafiya.

Ita ma kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta buka ci a gudanar da bincike don gano wadanda ke da laifi a arangamar.

Shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya ce kungiyar ta damu matuka da kashe-kashen da aka samu, sannan ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba da irin haka ke faruwa a kasar.

Farfesa Abdullahi ya ce tawagar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika don duba abin da ya faru ta yi kadan, inda ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya ce zai kafa hukumar bincike game da lamarin.288