Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Laraba

16 Disamba 2015

03:42:08
725152

Dalilin sojoji na afkawa 'yan uwa a Zariya - "Abin dariya" yaro ya tsinci hakori

Kungiyar kula da hakkin musulmi [MURIC] ta bayyana dalilin da Sojojin gwamnatin Nigeria suka rike na afkawa Harkar Musulunci a Zariya, a matsayin wani abin dariya, inji Bahaushe wai yaro ya tsinci hakori. Sojojin Nigeria sun fake da cewa wai 'yan uwa sun nemi halaka shugaban sojojin Nigeria ne Lt. General Burutai

Amma sai ya tsallake rijiya da baya, saboda haka nan su kuma sai suka dauki wannan matakin na kisan dubban al'ummar musulmi 'yan uwa.

Jaridar Turanci Daily Trust ce ta dauko wannan labarin sannan ta ci gaba da bayanin cewa babban daraktan kungiyar ta MUNIC Professor Ishaq Akintola ya bayyana cewa Harkar Musulunci tana da tarihi na kiyaye zaman lafiya da gudanar al'amurran su cikin kwanciyar hankali, saboda haka nan wannan harin na sojoji ba shi da wani dalili.

Ga wani yanki na shafin wannan jarida:288