Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nigeria
Laraba

16 Disamba 2015

03:14:03
725150

Jama'ar Sayyid Muqtada Sadr na Iraki sun fara shirin gagarumin gangami a kasar

Babu shakka al'amarin ta'addancin sojojin Nigeria akan Harkar Musulunci a Nigeria da kutsen da suka yi a gidan jagoran Harkar Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky wanda yayi sanadin shahadar dimbin 'yan uwa da jikkitar da dama, abu ne da ya ja hankalin dukkanin duniya a yanzun

Daya daga cikin malamai a kasar Iraki kuma sanannen mai fafatawa da rundunar mamaya a kasar Sayyid Muqtada Sadr sun fara shirin gabatar da gagarumar muzahara a kasar.

Yanzun haka dukkanin yankunan da mabiyan sa suke sun fara daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna nuna goyon bayan su gare shi da kuma yin Allah waddai kan abin da sojojin gwamnatin Nigeria suka yi ma shi.288