Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Talata

15 Disamba 2015

08:34:59
724988

Ayatullah Akhtari yayi kakkausan suka kan hare-haren sojojin Nigeria a Zariya

Shugaban kungiyar Ahlul Bait na duniya Ayatullah Muhammad Hassan Akhtari ya yi kakkausan suka akan hare-haren sojojin Nigeria a Zariya, wanda ya kai ga kasha dimbin almajiran Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da kuma yin kutse gidan babban malamin a unguwar Gyallesu a cikin garin na Zariya.

Ayatullah Akhtari yayi wannan kakkausan suka ne a wata hira da yayi da gidan Talbijin an Al-Alam Iran, yana mai cewa kai hari akan Husainiyar Baqiyyatullah da kuma gidan Malam a unguwar da yake zaune abin tir ne da Allah waddai. 

Ayatullah Akhtari tare da bayyana bakin ciki kan abin da ya faru ya yi kira ga sauran al'ummar duniya da su nuna damuwar su, da kuma goyon bayan al'ummar musulmi da aka zalunta a garin na zariya.288