Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : BBC
Litinin

14 Disamba 2015

20:02:36
724931

Sojoji;Matar Shakh El-Zakzaky na nan da ranta

Rundunar sojin Nigeria ta musanta rahotannin da ke cewar an kashe mai ɗakin jagoran 'yan uwa musulmi na kasar, Malama Zeenat Ibraheem.

Shugaban rundunar sojin a Kaduna, Manjo Janar Oyebade wanda ya sanar da hakan ga manema labarai ya ce, a yanzu haka shugaban kungiyar ta Islamic movement, Malam Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Malama Zeenat na hannun jami'an tsaro kuma suna cikin koshin lafiya.

A ranar Lahadi ne, yan uwa suka bayyana cewar an hallaka Malama Zeenat tare da wasu manyan shugabannin kamar, Malam Turi da kuma Malam Ibrahim Usman.

Ana ci gaba da zaman zullumi a yankin Gyallesu inda gidan El-Zakzaky yake a birnin Zariya a yayin da kuma ake zargin jami'an tsaron sun hallaka mabiya kungiyar da dama.

Sojojin kasar sun zargi kungiyar ta Shi'a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da ya je Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.288