Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Litinin

14 Disamba 2015

16:29:48
724887

Hukumar kare hakkin dan adam "IHRC" ta nemi sanin halin da Malam ke ciki da lafiyar sa

Hukumar kare hakkin dan Adam ta musulunci dake da mazauni a kasar Britaniya ta nemi sanin cikakken halin da jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky yake ciki da kuma yanayin lafiyar sa, tun bayan rahotannin da suke nuna cewa sojojin gwamnatin Nigeria sun isa gidan kuma sun kutsa ciki

A wata takarda da suka rabawa manema labarai hukumar ta yi bayanin halin da ake ciki tun bayan soma hare-haren na sojoji da suka fara a ranar Asabar din nan data gabata, wanda kuma ya ci gaba har zuwa yau Litinin a bangarori daban daban na garin na Zariya.

A wani bangare na takardar da suka rabawa manema labarai sun yi bayani sosai kan isar sojoji da muggan makamai gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da dukkanin irin abubuwan da suka auku na keta hakki.

Saboda haka nan suka yi kira da babbar murya cewa alhakin lafiyar Malam yana hannun gwamnatin kasar Nigeria ne.

Irin wannan kiraye-kirayen ne kuma malamai da masana a kasashe daban daban suke yi na nuna damuwar su da sanin hakikanin lafiyar Sheikh El-Zakzaky.288