Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Litinin

14 Disamba 2015

16:21:18
724885

An kirayi 'yan uwa musulmi da su ci gaba da daukan mataki ba tare da yankewa ba

An kirayi 'yan uwa musulmi a ko ina suke da su ci gaba daukan mataki cikin tsari da aka san su da shi, ba tare da yankewa ba kan irin halin da muke ciki tare da bin matakan hawa - hawa don tabbatar da cewa mun kai ga bukatun mu, da cimma hakkokin mu na kare jagoran mu Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky

Kiran da ya fito ne daga kwamitin 'yan uwa masu gudanarwa a yanzun, wanda ya nuna cewa kamar yadda aka fara da gabatar da muzaharori na lumana akan manyan titunan kasar nan tun daga ranar Asabar da dare, har zuwa wayewar garin ranar Lahadi, ya kamata ne a ci gaba da daukan matakai daban daban har zuwa lokacin da zamu cimma hakkin dake kan mu na kare jagoran mu. 

Babu shakka tun lokacin da sojoji dauke da manyan makamai suka isa gidan Sheikh El-Zakzaky rayuwar sa da ta iyalan sa suke cikin hadari, kuma hakkin mu ne ganin mun basu kariya gwargwadon ikon mu.

Alhamdullah daukakin al'ummar musulmi a ciki da wajen Nigeria suna shaida akan dukkanin irin kisan rashin tausayi da sojojin gwamnatin Nigeria suke yi akan al'umma wadanda babu komai tare da su, ba domin sun yi laifin komai ba, haka nan kuma al'umma suna ganin yadda aka cinnawa gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria wuta, wani bangare na gidan ya kone kurmus.

Tare da kutsawa cikin gidan da harbe dukkanin wadanda aka iya gani.

Sannan bai buyawa al'umma ba irin yadda aka jefa abubuwa masu fashewa a cibiyar addini watau Husainiyar Baqiyyatullah, alhali a cikin ta a lokacin akwai mata da yara wadanda suka hallara don shaida taron bukin daga Tuta koriya da musanya ta da baka saboda shiga watan alfarma na Maulidin Manzon Allah[SAWA], Wanda yayi sanadin shahadar dimbin mutane tare da jikkita wasu masu yawa.

Haka nna kuma al'umma suna shaidar yadda aka kashe likita mai kula da wadanda suka ji rauni, sannan aka rika hana isar da taimakon agaji ga masu bukata.

Don haka nan muna da hakki mu fito mu nuna rashin amincewar mu kan dukkanin wadan nan keta hakki, tare da Neman bin hakkin mu kamar yadda kowa yake da shi.288