Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Harkar musulunci a Nageria
Litinin

14 Disamba 2015

04:43:37
724764

Wasu hotunan kisan da sojoji suka yi a gaban gidan Malam da kona wani sashi

Kamar dai yadda rahotanni da labarai suka bayyana sojojin gwamnatin Nigeria sun isa gidan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky inda suka kona wani sashi na gidan sannan kuma suka kasha dukkanin wanda suka tarar a kofar gidan suna tsaro, su kayi abin da suka ga dama na keta hakki

Abin da al'umma suke ta tambaya bayan ganin irin wannan abu shine me gwamnatin Nigeria ke nufi da wannan abu? Ashe ba akwai dokoki a kasar ba? Me zai sa ba za'a kama mai laifi a kai shi gaban kuliya ba, a tabbatar da laifin sa kuma a hukunta shi? me yasa dukkanin wannan abu? Me yasa Husainiyar Baqiyyatullah? Me yasa gidan Malam a Gyallesu? kuma me yasa wajen hada film din rayuwar mujaddadi Shehu Usman Bn Fudiyo [RA] a Darur Rahamah?

Ga wasu hotunan keta hakkin dan adam a Gyallesu:288

zaria

zaria

zaria

zaria

zaria