Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : BBC
Lahadi

13 Disamba 2015

15:36:25
724667

Yayin da al'amura ke ci gaba da dagulewa tsakanin sojan Najeriya da kuma 'yan uwa musulmi a Zaria, rahotanni na cewa, an kashe mukaddashin jagoran 'yan uwa a Najeriya Malam Muhammadu Turi.

Kafin dai kisan Malam Turi shi ne ke jagorantar 'yan uwa a Kano.

Rahotanni daga sassan Nigeria na cewa, 'yan uwa musulmi karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim El Zakzaky suna ci gaba da zanga-zanga a biranen Nigeria da dama da suka hada da Katsina, da Kano da kuma Potiskum.

Jiya ne dai aka soma wannan yamutsi, inda rundunar sojan Najeriya ta zargi 'yan uwa da kokarin halaka babban hafsansu Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai yayin wata ziyara a Zaria.

Amma 'yan uwa sun musanta zargin da sojan Najeriyar suka yi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tun kusan lokacin sallar Azahar aka fara rushe gidan na Sheikh Al-zazzaky, kuma duk da a yanzu kura ta dan lafa, akwai bayanai dake nuna cewa hayaki na tashi a gidan kuma tuni aka rushe shi.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce an rushe Husainiyya, da kuma wasu marakiz 'yan uwa musulmi.288