Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : BBC
Asabar

12 Disamba 2015

20:34:30
724522

Ba mu muka kai wa Burutai hari ba — Zakzaky

'Yan uwa Musulmi mabiya mazhabar shi'a a Najeriya, sun musanta zargin kokarin halaka shugaban dakarun kasar Laftanal Janaral Tukur Yusuf Buratai.

Shugaban Harkar musulunci na Nageria Sheikh Ibrahim El-Zazzaky na cewa, babu wani daga cikin mutanen mu da ya yi kokarin kai hari ga wani Soja, ballantana ma shugaban na Sojoji.

Har yanzu ba ta tantance mutanen da aka halaka da kuma raunata ba a wani hari na babu gaira babu dalili yayin bikin canza Tutar da ‘yan uwa su kan yi duk shekara.

Rundunar ta Sojojin na Najeriya ce dai ta shaidawa BBC cewa mabiya mazhabar Shi'a sun yi kokarin halaka Laftanal Janaral Buratai a wata arangama a Zaria.288